18 Yuli 2016 - 13:37
Sojojin Syria Suna Ci Gaba Da Kwace Yankunan Da Suka Rage A Hannun 'Yan Ta'adda A Aleppo

Dakarun gwamnatin kasar Syria suna ci gaba da kara nausawa a cikin yankunan gundumar Aleppo da ke hannun 'yan ta'adda a daidai lokacin da Turkiya ta shagaltu da batun juyin mulki.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, sojojin gwamnatin kasar ta Syria sun samu manyan nasarori a cikin 'yan kwanakin nan musamman bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiya wanda bai yi nasara ba, inda a halin yanzu gwamnatin Turkiya ta shagaltu da matsalolinta na cikin gida.

A nasa bangaren shugaban kasar Syria Bashar assad ya bayyana cewa, dauki ba dadin da ake yi a haln yanzu tsakanin dakarun kasar da kuma 'yan ta'adda a Aleppo shi ne zai fayyace makomar kasar a siyasance da kuma ta fuskar tsaro, kasantuwar Aleppo ita babbar hanya da Turkiya ke kaiwa 'yan ta'adda dauki, wanda kuma yanzu an rufe mafi yawan hanyoyin.288