Hukuncin dake zuwa shekaru 25 bayan kifar da gwamnatinsa sakamakon wani juyin mulkin soja.
Murna ce ta barke tare da kuwace kuwacen dadi a cikin kotun bayan da alkali Bertao Gustave Kam, ya sanar da hukuncin daurin rai da rai ga Hussein Habre shekaru sama da 20 bayan aikata laifukan.
Wannan hukunci dai ya yi la akari ne da irin laifukann da aka tabka daga 1982 zuwa 1990 lokacin Hussein Habre ya shugabancin kasar ta Cadi, bayan wulakantawa tare da kisan dimbin yan adawa, da kabilun kudancin kasar da yake zargi da taimakawa yan tawayen dake yakar gwamnatinsa .
Bincike a cikin takardun hukumar yan sanda kasar ta Cadi DDS Sun gano wasu takardu na mutane dubu biyu da dari biyar da shugaban Habre da kansa ya sa aka hallaka su, baya ga wadanda aka tsare babu shara’a ,
Bayan hukuncin habre bai ce kala ba sannan alkali ya bashi kwanaki 15 idan bai yarda da hukuncin ba ya daukaka kara.288