Shugabannin kasashen Amurka, Britania, Faransa, Jamus , Italia, Canada da mai masaukin baki Japan ke halartan tattaunawan a yankin tsaunukan Ise Shima mai nisan kilomita 300 kudu maso yammacin birnin Tokyo.
An dauki tsauraran matakan tsaro a fadin kasar ta Japan, inda aka girka ‘yan sanda na musamman a tashoshin jiragen kasa da wurare masu muhimmanci gudun kada a fuskanci wata matsala.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa ba zasu yi sake ba ganin irin barnan da ‘yan taadda sukayi a Paris da Brussels cikin shekarar data gabata.288