Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin fararen hula sun kaddamar da zanga-zanga domin adawa da ‘Yan majalisun Najeriya da suke zargin suna zagon kasa ga samun nasarar aiwatar da kasafin kudin bana a Najeriya.
Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu yace ba za su iya fada da shugabansu ba amma suna iya jayayya da shi kan bukatun da suke ganin ya dace a gyara.
A jiya Talata Masu zanga-zangar sun toshe hanyar zuwa Majalisa a Abuja tare yin kira ga shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki ya yi murabus.
Ndume yace babu wata girman zanga-zanga da za ta sa wani Dan Majalisa ya yi murabus. A cewar shi Zanga-zangar ta sabawa tsarin mulki domin akwai tsarin kiranye da ake yi akan duk wani Dan Majalisa.