31 Maris 2016 - 13:26

Jiragen Saman Yakin Kasar Rasha Sun Kashe 'Yan Ta'addan Da'ish Fiye Da 60

A ci gaba da hare-haren da jiragen saman yakin kasar Rasha ke kai wa kan sansanonin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish masu kafirta musulmi a kasar Siriya, jiragen sun halaka 'yan ta'adda akalla 60 tare rusa sansanonin masu yawa.

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha a cikin daren jiya Laraba ta sanar da cewa: Jiragen saman yakin kasar sun kai wasu jerin hare-hare kan sansanonin mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish guda hudu a sassa daban daban na kasar Siriya, inda suka kashe 'yan ta'adda akalla 60 tare da rusa sansanonin.

Har ila yau hare-haren sun tarwatsa tankokin yaki da manyan makamai masu kakkabo jiragen sama da kuma rumbun tsimin man fetur na 'yan ta'addan a cikin kasar ta Siriya.

A bangare guda kuma rahotonni sun bayyana cewa; a cikin mako guda kacal hare-haren jiragen saman yakin kasar Rasha sun yi sanadiyyar halakar 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish fiye da 500 a kasar ta Siriya.288