Ana saran shugaba Buhari zai hadu da shugaba Barack Obama da sauran wasu shugabannin kasashen duniya 60 da ke halartar taron.
Taron dai zai tattauna a kan takaita yaduwar makaman nukiliya, inda ake saran shugaba Buhari zai jaddada matsayin Najeriya na goyon bayan kasashen duniya a kan amfani da nukiliya don samar da makamashi da kuma ci gaba.
Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Najeriyar ta ce, a yayin ziyarar, shugaba Buhari da wa su gwamnoni da ke rufa masa baya za su tattauna batutuwa daban-daban da manyan jami'an gwamnatin Amurka da kuma sauran shugabannin kasashen da ke halartar taron.288