Shugaban wanda ya gudanar da taron gangaminsa na karshe marecen jiya a birnin Yamai, ya ce zai yi nasara ne sakamakon irin ayyuka na ci gaban kasa da ya aiwatar a cikin shekaru biyar da suka gabata.
To sai dai abokannin hamayyarsa na siyasa sun ce ba ta yadda Issoufou Mahamadou zai yi nasara a zagayen farko na wannan zabe.
Yanzu haka dai akwai ‘yan kallo daga cikin da kuma wajen kasar wadanda hukumar zabe ta bai wa izini sa-ido kan yadda zabe na jibi zai gudana.288