28 Janairu 2016 - 14:46
Iran Ta Ce Wajibi Ne A Hana "'Yan Ta'adda" Halartar Taron Sulhun Kasar Siriya

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan lamurran da suka shafi kasashen Afirka da na larabawa Husain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewar kai kamata a bar 'yan ta'adda da suka sanya sanya rigar 'yan adawa su halarci taron sulhu tsakanin gwamnati da 'yan adawan kasar Siriya ba.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar Husain Amir Abdullahiyan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a ci gaba da ziyarar da yake yi a kasar Rasha inda ya ce: Bai kamata a bar 'yan ta'adda da suka lullube fuskokinsu (da sunan su ma 'yan adawa ne) su zauna teburin tattaunawar da za a yi tsakanin tawagar gwamnatin Siriya da na 'yan adawa a nan gaba.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran yana mayar da martani ne ga matsin lambar da gwamnatin Saudiyya take yi wajen ganin sai a shigar da wasu kungiyoyin na 'yan ta'adda cikin jerin tawagar 'yan adawan da za su zauna da tawagar gwamnatin Siriya don tattauna hanyoyin da za a kawo karshen rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar.

Husain Amir Abdullahiyan ya kirayi gwamnatin Saudiyya da ta kawo karshen irin goyon bayan da take ba wa 'yan ta'addan Siriyan wanda ke kara ruruta wutar yakin basasan da ke faruwa a kasar Siriyan.288