20 Janairu 2016 - 15:10
MILLOLI DA AQEEDU NA 13

Shaikh Hamzah Muhammad Lawal BABIN HALASCIN TSINEWA YAZID DA BANU UMAYYAH

To muna cewa(hadisan) sun cika sharuddan Bukhari da Muslim,kamar yadda Al-Maqdasi yake fadi a cikin littafin shi mai suna SHURUDUL A’IMMAL KAMSA,wato sun cika sharudda amma kuma basu zo da hadisan ba,shi kuma ko ya zo dasu kuma ingantattu ne.
Kuma in Allah yaso in muka zo muna magana akan Imamul Bukhari zata bayyana akan cewa bai zo da dukkan ingantattun hadisai ba,kuma shima bai yi da’awan cewa yazo dasu gabaki daya ba domin da kan shi yana cewa : WAMA TARAKTU MINAS SAHIHI AKSAR .
Al-Hakim yana cewa daga Abi Barzak cewa :
“KANA ABGADU ILAR RASULILLAH {SAW} BANU UMAYYA, WA BANU HANIFA WA BANU SAQIF” ma’ana Mafi kyama a cikin mutane ga Manzon Allah {saw}wato wadanda Manzon Allah {saw} yafi fushi dasu sune Banu Umayya…..Kuma kun san Manzon Allah {sawa} baya fushi don kan shi.In ka duba Dabaqat na Ibn Sa’ad zaka ga inda A’ishah take cewa Manzon Allah {sawa} ya kasance baya fushi domin kan shi saidai idan aka keta alfarman Allah,ka duba Dabaqatul Kubra zaka ga wannan.
Saboda haka Banu Umayya sune wadanda Manzon Allah yafi fushi dasu a cikin al’ummah gaba daya,cewa  yayi Manzon Allah : “KANA ABGADAN NASI AHYA’AN ILALLAHI BANU UMAYYA.Saboda wadanda Manzon Allah yafi fushi dasu a cikin masu rai gabaki daya sune Banu Ummayya da Banu Hanif da Saqif.
Sannan sai Yace:wato Tahaqiq din Hakim,sai yace HAZA HADISUN SAHIHUN ALA SHARDISH SHAIKHAIN,ma’ana wannan hadisi ne ingantacce a sharadin Bukhari da Muslim.Kuma wannan bayanin yana nan a cikin AlMustadriku Alas Sahihaini a Kitabul Fitni Wal Malaahim,daidai wajen yake cewa IZA BALAGAT BANU UMAYYA ARBA’INA,a wannan wurin zaka duba.
Sannan Ibn Hajar Al-Haisami ya rawaito shi a cikin Majma’uz Zawa’id din shi juz’i na 13.Sannan Qadul Qudat Abu Ya’ala shima ya rawaito shi.
Kuma mun gaya maku cewa daga cikin wadanda suka halasta tsine ma Yazid akwai shi wannan Qadul Qudat Abu Ya’ala shima ya tafi zuwa ga wannan ra’ayi din.Sannan akwai shi wannan bayanin a cikin المستدرك على الصحيحين للحاكم na Al-Hakim An-Nisaburi a wannan dai Kitabul Fitani wal Malahim din,a wurin Khudubatun Nabiy zaka duba.A nan wurin Al-Hakim yake cewa an rawaito daga Abu Sa’idil Kudri,Yake cewa Manzon Allah {sawa} Yace:“Hakika mutanen gidana za su samu kisa da korewa.Sannan wadanda za su fi kowa gaba dasu mutanen gidana din-inji Manzon Allah{sawa}-sune Banu Umayya da Banu Mugira da Banu Makzum”.Kuma sai Hakim din yace wannan hadisi ne sahihul isnad ma’ana wannan hadisi ne mai ingancin isnadi.
KANZUL UMMAL
Irin wadannan akwai su da yawa ban da lokacin da zan kawo sune amma ga wani hadisi daga Kanzul Ummal juzu’i na 6 shafi na 68.Yana cewa ya samo daga Bajjala yana cewa:Nace ma Imran Ibn Hussain,ba ni labarin wadanda Manzon Allah yafi fushi dasu a cikin mutane gabaki daya.To sai Imran din yace mashi in na gaya maka zaka kiyaye asirin ba zaka gaya wa mutane ba har sai na bar duniya?-wato Ya gindaya mashi sharadi cewa zaka rufe,kaki gaya ma kowa cewa nine masdar dinka,har sai nabar duniya?Sai yace mashi ee(wato zai kiyaye sharadi),to sai yace:Sune Banu Umayya da Banu Saqif da Banu Quraiza.Kuma irin wadannan suna da yawan gaske,akwai su a littafai kaman Kanzil Ummal da sauransu
Kafin mu shiga As-Suyudi bari muce a nan mai Kanzil Ummal ya rawaito daga Umar dan Kaddab a tafsirin wannan ayan inda Allah yake cewa:ALAM TARA ILALLAZINA BADDALU NI’IMATALLAHI KUFRAN AHALLU QAUMAHUM DARAL BAWAR,Sune wadanda suka canza ni’iman Allah zuwa ga kafirci-bawai kafirci na I’itiqadi ba.Cewa ba ku yi dubi ba zuwa ga wadanda suke canza ni’ima zuwa ga kafirci….Sai Ummar dan Kaddab yace:Sune mafi fajirci daga guda biyun nan,sune Banul Mugira da Banu Umayya.
Kamar yadda Allah yake cewa a cikin Suratul zukrif.
وَمَا نُرِيهِمْ مِنْ آَيَةٍ إِلَّا هِيَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا وَأَخَذْنَاهُمْ بِالْعَذَابِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ (48)-Haka muke so mu rinka kawo hujjoji-Bama nuna masu daga wata aya sai ta zama cewa tafi girma daga yar uwarta ta baya wadda muka kawo.Haka Musa {as} yake cema mutanen Fir’aun.UKT da ma’anar MISL,kamar in kace KANA WA AKHWATIHA wato KANA da yar uwarta.To!me kenan?Ma’anarta shine KANA WA MISALATUHA.Ukut anan da ma’anar uktiha,ko yar uwa da ma’anar misali.
Wato kowace aya aya muka kawo masu ta wadatar ba sai mun kawo masu na gabanta ba sai dai sun ki su yarda,to sai mu kawo masu nagaba itama irin ta kammalalla.Haka muka dinga doddorasu inji Musa{as] amma basu karba ba.
Daga karshe suka ce mashi ya roki Ubangijin shi-ba wai Ubangijinsu ba ubangijinshi sukace-Da ya roki Ubangijin nashi kuma daga karshe suka sake butulcewa.
وَمَا نُرِيهِمْ مِنْ آَيَةٍ إِلَّا هِيَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا
Sannan bayan haka yazo daga Ali{as} a cikin Kanzinzil Ummal din a tafsirin ALAM TARA ILALLAZINA BADDALU NI’IMATALLAHI KUFRAN….sai yace HUMUL AFJARAN shima iri daya da wancan.
AZ-ZAMAKSHARI AL-MU’UTAZILIY
Sannan Az-zamakshariy yazo dashi a cikin littafin shi Al-Kashshaf  a tafsirin a wannan ayan
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ بَدَّلُوا نِعْمَةَ اللَّهِ كُفْرًا وَأَحَلُّوا قَوْمَهُمْ دَارَ الْبَوَارِ (28)
Daga Umar dan Kaddab yace sune fajirai guda biyu,wato da Banu Umayya din kenan.Amma akwai wani hadisi guda daya da nake so in rufe dashi a wannan wurin.
Yazo a cikin Kanzil Ummal din dai daga Ibn Mas’ud yana cewa: “Kowane addini yana da musiba,musiban wannan addini shine Banu umayya(inji Ibn Mas’ud).To sai ya zama Zahabi ya yarda da wannan maganan.Wannan yana da muhimancin gasken gaske.
SHAMSUDDINIZ ZAHABI
Shamsuddiniz Zahabi ya ambaci wannan a cikin Mizanul I’itidal dinshi juzu’i na biyu shafi 181.Sannan sai ya inganta shi,yace hadisi ne ingantacce.Wannan yana da muhimmancin gaske.Wadanda suke sa shakka akan ingantawan AlHakim AnNisaburi,kamar Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah.Yana(wato Ibni Taimiyyah) cewa Hakim na saurin cema hadisi ingantacce.To wani lokaci Zahabi na zuwa yai muwafaqa da AlHakim din.Wannan muwafaqan Zahabi din tana da muhimmancin gasken gaske-Ku rike wannan a bahasosi akan hadisai.288