17 Janairu 2016 - 11:51
IS sun hallaka mutane 300 a Syria

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria ya rawaito cewa mayakan IS sun hallaka fararen hula 300 a wani kauye da ke gabashin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa yawancin wadanda aka hallaka a kusa da birnin Deir al-Zour mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi.

Kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da Syria wato IS, ta bullo da sabbin hanyoyin kai hare-hare a gundumomin da gwamnatin Syria ke iko da su da kuma birane.

Wasu rahotannin sun ce an hallaka dakarun gwamnati da fararen hula a wasu biranen kasar.

A bangare guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai fargabar mutane 200,000 na fuskantar barazanar karancin abinci a Syria.288