25 Disamba 2015 - 13:24
TSOKACI DA SHAWARA DANGANE DA WAQI’AR ZARIYA NA 1

NA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL YUSUF SULAIMAN YA RUBUTA

A’UZU BILLAHI MINASH SHAINADIR RAJEEM BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM WASALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIREEN ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH WA BARAKATUH Suna na Hamzah Muhammad Lawal.Nine babban sakatare na Althaqalayn Cultural Foundation,wata mu’assasa wadda take ba ta hukuma ba,me regista da Corporate Affairs Commission of Nigeria mai numba CAC/IT/NO23222. Tsokaci game da abubuwan da suke faruwa a cikin wannan kasan musamman dangane da abubuwan da suka faru a Zariya a ranar Asabar da ta wuce 12/12/2015,daga wannan lokacin zuwa yau.Ittifakan daga cikin manufufin wannan Mu’assasa akwai tabbatar kyakykyawar zamantakewa tsakakkanin membobin ta da kuma al’umma gabaki daya kamar yadda yake ayyananne a cikin tsarin mulkin ita Mu’assasa din. Harshen mu a yau insha Allah zai zama harshen ishara da kuma nasiha.Ko da yake dawa daga cikin mutane sun san abubuwan da suka faru din saboda haka ba muna so bane a kara harzuka su mutanen ba ko abin da yayi kama da haka ba.Akwai kurakurai da yawa wanda muka ga cewa sun afku a lissafin mu,ko da yake zai iya zama muyi kuskure.A janibobi daban daban muna ganin kurakurai sun afku saboda haka muna so mu ankarar ga wadannan kurakurai,sannan mu yi bayani akan abubuwan da muke ganin zai iya zama warwara sannan kuma mu yi nasihohi  sannan mu bada shawarwari daidai gwargwado. Daga cikin manya manyan kurakurai wadanda muke ganin sun faru a janibin sojoji,wa’yanda suka zo wucewa zuwa DEPOT Zaria a wannan ranar :Akwai rashin sanin cewa su ‘yan uwa Musulmi suna da wata safga  akan wannan titin a wannan ranar- akan asasin wani hoto mai motsi da na gani wanda wani daya daga cikin sojoji wanda nake kaddara cewa shine Col Sani Kukasheka tun da ban san shi ba,akan asasin abin da na gani a wannan hoto mai motsin in da yake cewa wallahi bamu sani ba a lokacin da yake fadawa wadanda ya iske a wajen akan cewa su sun zo wucewa ne basu san cewa wani abu na faruwa ba kuma ba akan nufin fada suka zo wajen ba da su ‘yan uwan ba.Idan abin da muka gani a cikin wannan hoto mai motsi din ya inganta haka ne cewa “wallahi ba mu sani ba” to!wannan ba karamin kuskure bane,ya zama cewa Chief Of Army Staff na Nigeriya zai shigo cikin wani gari ya  bi wata hanya ayyananna amma gabaki daya sai ya zama rundunar sojan Nigeriya basu san abin da yake faruwa akan wannan hanyar ba,wannan ba karamin kuskure bane a awon mu ko lissafin mu. Ya kamata ya zama cewa akalla kwana daya ko da bai zama kwanaki ba kafin zuwan Chief of Army Staff cikin wannan garin ya zama cewa akwai abin da ake ce ma “INTELLIGENCE”dangane da yanayin da garin yake da kuma hanyoyin da za a iya bi da kuma options na hanyoyin da ababen da suka yi kama da wannan sai ya zama an fahimci cewa a wannan ranar akwai abin da zai faru a wurin sai ya zama an iya yin magana da su mutanen da abin ya shafa har a kai ga fahimta ta juna-ban so nayi magana mai tsawo akan wannan .Wannan shi a kankanshi ya isa ya zama zai iya jefa Chief Of Army Staff din cikin hatsari ko da ba da su ‘yan uwa ya hadu a rannan ko ba dasu ba,kawai dai kila ittafaq ne ko dacewa shi yasa abin ya faru a rannan amma zai iya faruwa da kowane ne,wannan kuskure ne babba ta janibin rundunar sojan Nigeriya gabaki daya.Akan wannan asasin in abin gaskiya ne kuma haka din ne ya faru cewa “wallahi basu sani ba”to!zamu iya cewa duk abin day a faru a wannan wurin a hankalce kuma mu yanke hukunci mu ce kawai KNEE JERK RESPONSE ne,KNEE JERK RESPONSE ne da ma’anar  wato ABRUPT,SUDDEN da kuma WITHOUT CAREFUL CONSIDERATION ko tunani ,wato kowa yana yin abin ne ba akan shiri ba,ba sojojin ba, basu ‘yan uwan ba,an yi arangama akan hatsari ya jawo abubuwa da jawo har zuwa yau kuma bamu san iyakar in da zai kai ba,wannan babban kuskure ne a janibin sojan Nigeriya kuma dole ya zama an bincike ya aka yi wannan barnar ta faru.Sannan shi kanshi COAS ya kamata ya binciki wannan cewa ya aka yi ya faru cewa zai biyo wuri amma kuma ba a san yanayin wurin ba.Wannan zai iya sa shi a kowanne irin hadari,hard a wannan hadarin daya faru,wannan kuma muna magana ne akan asasin MA’ALUMAT da suke a gaban mu,ba muna magana akan bincike mai zurfi bane ko abin da yayi kama da wannan ba amma dai wannan kuskure ne babba,na farko kenan. Sannan kuskure na biyu da muke gani daga janibin sojoji shine yanda suka yi mu’amala tare da yanayin da suka samu,wanda daga karshe mu’amalar ta kai ga wannan harbe harben da sauran abubuwa wanda aka yi.Domin karshe abin da zaka iya cewa idan ana ganin cewa akwai wani laifi wadanda aka iske suka yi shine sun tare hanya,sannan sun ce soja (wato COAS)ba za su wuce ba.Wannan laifi ne wanda yake karami NISBIYYAN wato RELATIVELY SPEAKING wato idan aka kwatanta shi da sauran nau’o’i na laifofika.Saboda haka akwai yanda ya kamata ya zama an yi mu’amala da irin wannan laifin,kila saboda wannan KNEE JERK REACTION din da muka yi magana a asali sai ya zama cewa kowa ya rasa BALANCE dinshi sai ya zama an yi abin da aka yi.Laifi ne wanda ba laifi babba-wannan abin takaici ne sosan gaske cewa su sojojin basu ma iya samun wani mutum babba a cikin ‘yan uwa musulmi wadanda zasu iya mu’amala dashi su fahimci juna ba kamar yanda shi wannan hoto mai mosti ya nuna wanda idan muka zo magana akan kurakuran ‘yan uwa musulmi din kila  ko tabbas mu kawo wannan.Yana da ban takaici sosai day a zama cewa su sojojin suna tambaya cewa da wa zamu yi magana?wato waye mutum mai hankali wanda zamu yi magana dashi?sai ya zama babu.Zaka iya cewa kawai tawagar COAS ta hadu ne da wasu wadanda TECHNICALLY za ka iya DESCRIBING ko TA’ARIFIN SU a matsayin AREA BOYS ,to! Kuma ya kamata da sun yi mu’amala dasu da mu’amalar AREA BOYS,tun da Shaikh Zakzaky a lokacin baya wannan wurin balle su ce shi ya umurci su wa’yannan ‘yan uwan suyi abin da suka yi,ba ya wurin a lokacin kuma KAD’AN baya wurin,saboda haka kila sun hadu da –bari mu kamanta su da AREA BOYS-wa’yanda suke rike da gwafa da sanduna da ababen da suka yi kama da wannan.Yanda ake yi da Area Boys ya kamata da haka suka yi ma wadannan,ya zama sun budewa kan su hanya sun wuce,shike nan al’amari ya kare,sannan suna iya STATIONING wasu sojoji a wuri domin su tabbatar ba a yi rigima ba.Meanwhile a lokacin kuma sai su yi kokari su nemi shi malam din su sanar dashi abin da yake faruwa,sannan sai ya zama an san yanda za a warware,to!amma sai ya zama ba haka ya faru ba,sai suka dauki abin da karfin gaske wanda yake karfin yana da rudarwa da dimautarwa wato kenan yayi DEFYING din tunani na hankali,wato kenan hankali ba zai iya karban irin wannan reaction din bad a suka yi ma Area boys ba.Har wannan zai iya sanyawa mutum ya fara tunanin gasgata su yan uwan,dan daman tuntuni suna da wannan tunanin kuma suna fadi akan cewa kamar sojojin Nigeriya suna da wata jikakka da kulli tsakanin ta dasu.Wannan zai iya sanya mutane su fara tunanin haka domin tare hanya kowa yana yi ba dan shi’a kawai,shi yasa idan muka zo bada nasiha za mu ce mutane ka das u ji dadin wannan ya faru saboda in dai laifin shine tare hanya,to!kowa yana tare hanya.Tare hanyan kuma a matakai daban daban tun daga mataki dan karami har zuwa manya manyan matakai ana tare hanya. Sannan kuma nuna kyaman shugabanni ko kuma sabawa a ra’ayi da hukumomi kowa yana yi,ba wai ‘yan shi’a ne ko kuma ‘yan uwa Musulmi kawai suke yin wannan ba kuma zan iya bada misalai kadan a nan wurin.Mun sani akan cewa ana yin gangami daban daban a cikin wannan kasar wanda kuma wannan gangamin yana kaiwa ga zuwa rufe hanyoyi har da manya manyan hanyoyi TRUNK A.EXPRESS WAYS ana blocking din su a cikin wannan kasar,kuma wadanda suke yi suna alfahari cewa suna yin wannan saboda suna nuna tasirin su da yawan su da izzansu da abin da yayi kama da wannan,kuma dabakoki na mutane daban daban suna yi,zan ba da misalai kuma misalai ne kawai ba su da wani ma’ana in banda ma’anar misali din. Na shedi-ba akan shiri ba-maukibobi guda biyu a manya manyan birane a Arewacin Nigeriya.Na shedi maukibi a Katsina lokacin mun je daurin aure muka rasa daurin auren saboda ittafaqan a ran nan ne 12 ga watan Rabi’ul Awwal a Katsina.Sannan na shedi irin wannan maukibin a Kano,gabaki daya ana rufe garin ne kusan,kuma ba abin da mutum zai iya,in ma mutum ya nemi yayi jayayya,kai ba zai yiwu ba ma ka iya jayayya ba,in kayi zaka iya rasa ranka,saboda da hamasa wadannan matasan suke yin abubuwan da suke yi. Sannan dan takara Muhammadu Buhari shi ma na taba shedan shi a Kano ba akan shiri ba lokacin siyasar 2011  ba yanzu ba,a lokacin ya rufe Kano gabaki daya.Sannan lokacin da ake rufe tafsirai kamar a nan Kaduna,duk lokacin da Shaikh Dahiru Usman Bauchi yake so ya rufe tafsiri a filin sukuwa na Kaduna.Garin kusan yana tsayawa ne cak,kuma su mutane suna yin alfari da cewa sun tsai da garin.Ba wanda yake ganin cewa wannan din laifi ne,ko ana ganin laifi ne dai,to ba a daukan mashi irin wannan matakin. Sannan kuma ban da haka kuma kamar Redeemed Christian Church Of God-in aka bi ta bangaren kiristocin da suke cikin wannan kasar –su ma suna yin wannan a Lagos,Lagos/Ibadan express way rufe ta ake kwanaki idan suna yin tarurrukan su,kuma ko wane ne mutum ba zai iya wucewa ba.Manya manyan shugabannin kasa ma na siyasa da sauran su membobi ne na wannan cocin kamar yanda suke membobi a kungiyoyi daban daban na addinai,saboda haka idan suka zo su ma suna bin abin da ake yi ne a wurin. Sannan ban da haka kuma ‘yan Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah da ‘yan Darika da mutane daban daban kowa yana yi,kamar masallatan ranakun juma’a ana hawa kan titi a nan garin Kaduna misali da sauran garuruwa wanda ana rufe har express way ana yin Sallah akai.Sannan in kana so ka je Jos ka bi ta Mararrabar Jos zaka ga ana Sallar Juma’ah akan titi da sauran su.Haka cocina su ma suna rufe tituna,sannan ban da rufe titi yanzu ma ana DIVERSION wato ana karkatar da mutane daga inda suke so su bi,a sa su su bi wata hanya dole har zai an gama wannan ibadar da ake yi ko ta Musulmi ko ta Kirista. Sannan bukukuwa,ko na aure,ko na walimar saukan Alkur’ani,bukukuwa daban daban ana yi a rufe tituna da unguwanni da wurare.Haka kuma party,mutane suna yin party wanda ma kila kana iya cewa ya zama baa bin kirki ba a wasu lokuta ba.Masu party suna rufe tituna. Sannan ban da wannan akwai POLLUTION na NOISE,ana yin abubuwa da yawa kaman a lokacin watan Ramadhan a lokutan sallolin dare musamman a goman karshe na Ramadhan,duka gari yana dauka ba wai garin ba,ko ina yana yi.Wannan ta janibin rufe titi kenan. Amma ta janibin bijire ma shugabanni,ko yi masu bore,ko saba masu,ko kuma sabawa da ra’ayin su hukuma,wannan ba wani abu ne wanda shima sunan shi Shi’anci,kowa yana yi.Na san cewa shugaban kasa Umaru Musa Yar’aduwa an mashi bore a Jos,an bi shi kaman za a jefe shi,da kyar aka kwace shi a lokacin da ya taba zuwa Jos.Sannan Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida su ‘yan uwa musulmin sun taba samun wata ENCOUNTER dashi a Masallacin Sultan Bello Kaduna ba wani abu da ya faru.Haka kuma shugaba Goodluck Jonathan shi ma lokacin da yake yin kamfen a wurare daban daban an jefe shi da pure water.Sarkin Zariya,Alhaji Shehu Idris lokacin da ake so a nada wannan gomnan wato gomnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’I an jefe shi(wato Sarkin Zariya),an jefi Alkalin Alkalai,da kyar aka fitar da su.Bukola Saraki a Ilorin da kyar aka kwace shi a Masallacin Idi. Sannan ban da haka a duniya banda Nigeriya,a duniya akwai Bill Clinton ana jefan shi da rubabben kwai da tumatir –wanda wannan shine gayan alama ta wulakanta shugaba a wa’yancan al’adun.Sannan Toni Blair bai iya yawu a titunan London-wannan ka gaya wa kowa –Toni Blair ba zai iya yawo ba a titunan London a yau saboda tsana da kyama da turawa suke yi mashi.Sannan lokacin da aka yi  CHILCOT INQUIRY akan yakin Iraq wanda Toni Blair ya bada izni sojojin Birtaniya suka tafi suka yi yakin a Iraq,da aka yi wannan CHILCOT INQUIRY din,Toni Blair a boye aka shiga da shi dakin bincike din saboda mutane sun yi dandazo suna jiran in ya zo su far mashi,saboda haka mutane ba kashe aka yi ba,sai da aka nemi hanya ta baya kuma da asuba dugu dugu aka shigar da shi. Sannan lokacin da Toni Blair ya rubuta littafin shi ya kasa yayi lunching din littafin,a boye aka yi,aka je aka sanya littafan a BOOK SHOPS da sauran wurare sai mutane suka je suna koshe su suna canja masu in da aka sa su.Generori da masu uniform da yawa a duniyan nan a kasashe ba irin na mu ba zaka same su cewa suna shiga jirgin kasa,a jirgin kasa suke zuwa aiki sannan jirgin kasa suke dawo wa musamman a kasashen gurguzu kamar Tarayyar Soviet a da,da Rasha a yanzu da sauran su da sauransu. Saboda haka don an kai wa COAS hari in ka dauka cewa harin aka kai mashi ko an jefe shi misali,ko an yi abin da yayi kama da wannan,wani abu ne wanda yake OUT OF THE ORDINARY musamman saboda a yanzu a nan ana yin Demokradiyya ne wato ana yin mulkin farar hula,mutane suna da hakki akan bayyana ra’ayin su wato hakkin TA’ABIRI ma’ana FREEDOM OF SPEECH,abin da ake kokari shine ka da ya wuce gona da iri,saboda haka akwai kuskure babban gaskengaske ta wannan janibin a kan cewa mutane saboda sun tare titi sai ya zama sakamakon su  shine wannan.Wannan ya kamata a kalle shi sosan gasken gaske saboda zai iya jawo hadura masu yawan gasken gaske. ….akwai cigaba.288