Yawancin jihohin kasar na cikin matsalar rashin man Fetur din, inda daruruwan motoci kan dasa dogon layi a gidajen Mai.
Wasu daga cikin gidajen Mai dai na garkame ne saboda rashin man, ya yin da a wasu garuruwan jihar Adamawa Lita daya ta mai ta kai Naira dari da tamanin a wasu gidajen Mai.
A birnin Tarayya Abuja kuwa, layin mai har Zobe ya ke yi, inda wasu masu ababen hawa kan kwana su Hantse a layin mai ba tare da an zo kan su ba. Kusan watanni biyu kenan aka shafe ana fama da matsalar karancin man Fetur a Najeriya.
Ko a watan da ya gabata a rahoton da Bankin Duniya ya fitar kan tattalin arzikin kasar ya shawarci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da a cire tallafin Mai, a cewar bankin dawainiyar Tallafin Man ta fi alfanunsa yawa.288