6 Disamba 2015 - 15:01
An kai hari Bam birnin Aden na kasar Yemen

Wani bam ya tashi a birnin Aden da ke kudancin kasar Yemen, inda ya hallaka gwamnan birnin.

Kungiyar yan ta’adda ta da’ish wadda akafi sani da IS ta dauki alhakin kai harin da ya hallaka masu tsaron lafiyar Gwamnan da dama.

Gwamna Ja'afar Mohammed Sa'ad na sahun gaba-gaba a masu marawa dakarun gwamnatin Yemen baya wadanda suka yaki da mayakan  kabilar Houthi

Ya yin da tsohon shugaban kasar Abdrabbuh Mansour Hadi ya ayyana Aden a matsayin babban birnin kasar na wucin gadi a watan Yulin da ya wuce.

'Yan gabilar   Houthi na zaune ne a arewacin kasar, kuma sun karbe iko da yawancin sassan Yemen ciki kuwa har da birnin Sanaa288