22 Nuwamba 2015 - 10:22
Yan' ta'adda sun kashe wani malamin shi'a a Falestin

Wani mashahurin malamin shi'a a Falestin yayi shahada sakamakon harbin da wani mahari yayi masa.

Kamfanin dillanci labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-wasu mahara wadanda ba a san ko suwanene ba sun kai ma wani malamin shi'a hari inda suka harbai da bindiga wanda haka yayi sanadiyar shahadar sa.

Shaikh Ahmad shahwan dan shekara 75 mazaunin garin iksal kusa da alnasra wanda ke cikin yankin da yahudawa suka mamaye na Falestinawa ya hadu da ajalinsa ne ranar Juma'a da ta shude, shedun gani da ido sunce; an kama malamin hari ne lokacin da yake shagonsa na sayarda litattafai wanda nan take yace ga garin ku nan.

An bada hutun game gari a yankin da abun ya faru sakamako wannan rashi da a kayi. 288