Gamayyar kasashen da Amurka ke jagoranta na taimaka musu ta hanyar kai hare-hare ta sama.
Idan dai aka sake kama garin na Sinjar, za a hana 'yan kungiyar IS da ke yankin Raqqa da na Mosul ganawa da juna.
Dubban mabiya addinin Yazidi da ba su da rinjaye ne suka makale a garin lokacin da suka tsere kan duwatsun da ke Sinjar bayan dakarun IS sun kwace garin a bara.
An kashe daruruwan mutane, akasarinsu maza, sannan aka rika yin lalata da mata mabiya Yazidi.
Hare-haren da ake kai wa a kan garin Sinjar na daya daga cikin dalilan da suka sa Amurka ta fara kai hare-hare ta sama a yankunan da ke hannun kungiyar IS a Iraki a watan Agustan shekarar 2014, a daidai lokacin da ake ta gargadin cewa ana yin kisan kare-dangi a garin. 289