4 Satumba 2015 - 13:24

A ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da sojojin kasar Saudiya da kawayenta ke kaiwa kan kasar Yaman makayan kasar ta Yaman sun kai hari kan sansanin sojojin kawancen Saudiya kuma sun kashe sojojin hadadiyar daular larabawa masu yawa tare da wargaza jirgin saman yakin su, majiyar labaran sojin hadaddiyar daular larabawa ta tababtar da kshe sojojinta guda 22 tare da tarwatsa makansu masu yawa,

Mayakan kasar Yaman sun kashe wasu sojojoin hadaddiyar daular larabawa tare da tarwasta jirgin saman yaki kira Abachi mallakinsu.

A wata sanarwar da hedkwatar tsaron hadaddiyar daular larabawa ta fitar ta tabbatar da kashe sojojinta guda 22 a lokacin da mayakan kasar Yaman suka kai musu hari a lokacin da suke kokari kai hari a kasar, anasu bangaren mayakan na kasar Yaman su bayyana cewa sun kai hari kan gugun sojojin hadin guiwa da saudiya ke jagoranta wajen kai hare-haren wuce gona da iri a kasar Yaman kuma sun kasha da dama daga cikinsu,

A wani bangaren kuma dakarun sojin kasar Yaman da hadin guiwar dakarun sa kai na kasar sun kai hari kan tankokin yaki da wsu kayyakin yaki na sojojin kasar Saudiya a yankin Nasr da Kaab Jabiri da hakan ya jawo musu mummnunar Asara,

Ana ta bangaren hukumar bada agaji na majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa tana sauraron isar wasu kudade domin fara bincikin jiragen ruwan da ke dauke da kayyakin agaji domin taimakawa alummar kasar Yaman da yake ya yi wa yankar kauna288.