Minstan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa dangantaka tsakanin kasarsa da Kasar Ghana za ta kara habaka.
Minista Javad Zarif ya fadi hakan ne a wajen taron manema labarai da ministocin kasashen guda biyu suka gudanar a wata ziyara da ministan harkokin wajen kasar Ghana Hana Sarwatate ta kawo nan birnin Tehran, zarif ya kara da cewa idana kasashen biyu suka yi aiki da yarjejeniyar karfafa hulda tsakaninsu da suka ciamma daidaito akai alakar dake tsakaninsu za ta kara bunkasa sosai.
Ana ta bangaren itama minister kasar ta Ghana madam Hanna ta bayyana irin dadaddiyar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu kana ta nuna cewa suna jinjinawa kasar Iran game da nasarar da suka samu wajen cimma yarjejeniya da ta cimma da manyan kasashen turai guda 5 gami da kasar Jamus game da shirinta na nukiliya da aka dade ana cece kuce akai. hakazalika kamar yadda yake muna bukata kara fadada dangantakar mu da kasar Iran a fagagen tattalin Arziki, siyasa,ilimi da alaadu.
Daga karshe ministocin kasahen biyu sun nuna damuwa game da matsalolin rashin tsaro da wasu kasashen Afrika ke fuskanta sakamakon bullar kungiyar masu tsatstsauran ra’ayin Addinin ta Boko Haram, amma kasar Ghana ta yi amfani da mataken da suka dace wajen kare iyakar kasar daga sharrin yan taaddan288.