15 Agusta 2015 - 20:10

A yau ne aka bude taron kasa da kasa na cibiyar Ahlul baiti karo na 6 anan birnin tehran inda sama da baki 700 suke halarta daga kasashen duniya daban-daban da yake bayani a wajen taron shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya nuna cewa iran ba ta nufin hada kai da wasu kebantattun mutane tana nufin hada kai da dukkan musulmin duniya ne baki daya.

A yau ne aka bude taron cibiyar ahlul baiti na kasa da kasa karo na 6 anan birnin Tehran na kasar Iran da ya samu halartar baki sama da 700 daga kasashen duniya daban-daban.

A lokacin bude taron babban mai jawabi a wajen shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya jaddada game da muhimancin tunkarar barazanar da muke fuskanta daga masu karkataccen ra’ayin Addini, ya nuna cewa jamhuriyar musulunci ta iran babbar abin misali ce na irin yadda ta kirkiro sabon salo na tattaunawa da kowa.

Har ila yau shugaba Rohani ya kara da cewa jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta nufin hada kai da wasu kasashen kebantattu tana nufin hada kai da dukkan kasashen musulmi ne baki daya ba tare da wani bambanci ba, kuma ya zama wajibi mu hada karfi da karfe domin kalubalantar barazanar yan ta’adda da muke fuskanta.

Daga kareshe ya nuna cewa jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamina’e ya koya mana yadda za mu tattauna da kowa, don makarantar Ahlul baiti itace fassara hakikanin Addini, kuma wannan adinin musuluncin shi ne ya kulla alkawari da yahudawa da kiristoci, da kafirai, Kuma ya tsaya akan alkawarin.288

.