24 Yuli 2015 - 12:51
 Dan bidinga ya kashe mutane a Amurka

A kasar Amurka wani mutum mai shekaru 58 a duniya ya buda wuta a cikin wani gidan sinima inda ya kashe mutane biyu sannan ya raunata wasu 7, kafin daga bisani ya bindige kansa.

Wannan lamari dai ya faru ne a garin Lafayette na jihar Lousiana a kudancin kasar, a daidai lokacin da shugaba Barack Obama ke fara ziyarar aiki a yau juma’a a kasar Kenya da ke nahiyar Afirka.
Akalla jami’an tsaro dubu goma ne aka baza a birnin Nairobi, yayin da za a dakatar da tashi da kuma saukar jiragen sama na gajeren lokaci a birnin, da kuma rage karfin layukan waya a lokacin ziyarar.288