Kakakin hukumar, Leo Dobbs ne ya bayyana hakan, yana mai yin gargadin cewa lamarin ya faru ne sakamakon sabbin hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa a arewacin Najeriya.
A cewar sa, a 'yan makonnin da suka gabata, 'yan gudun hijira 30,000 ne a sansanin da ke Minawao, amma yanzu kusan kullum sai karuwa suke yi.
Ya yi kira a dauki kwakkwaran mataki na murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram domin mutane su ci gaba da zama a gidajensu.288