Watanni biyar da faruwar wannan lamari har yanzu hukumomi a Jamhuriyar Nijar ba su bayyana jirgin kowace kasa ba ne ya kai wannan harin.
To sai dai wani lauya mai zaman kansa Maitre Larwana Abdourahman a birnin Yamai, ya gana da ‘yan uwan mutanen da lamarin ya shafa kuma yana shirin shigar da kara a gaban kotun kasashen Ecowas ko Cedeao da ke birnin Abuja a Tarrayar Najeriya.288