Wata rana Mala’ika Jibril ya kawo wa Manzon Allah(saw) kasa daga kasan karbala ya sanya kasan a cikin kwalba ya baiwa Ummu Salma yace ta rike a hannunta duk randa ta ga wannan kasa ta koma jini to an kashe Imam Husain (as) sannan Manzon Allah yayi MA’ATAM wato makokin kisan Imam Husain,sannan Imam Ali ma ya yi Ma’atam akan asasin labartanwan Annabi sannan Imam Husain a lokacin da zai fita zuwa karbala da Ummu Salma take ce mashi kada ya fita ta kara da cewa Manzon Allah ya bata labari za a kashe shi a wurin sai ya bata amsa da cewa na fi ki sanin wannan labarin in kina so zan kara maki wata kasan akan kasan da Manzon Allah ya baki ki hada su zama kwalba biyu.To duk da wannan idan kayi bakin cikin a wannan ranar kayi bid’a kayi kama da yan shi’a ya wajaba a kaurace maka,shi yasa mutum ba zai iya ganewa ba idan ya ga yan shi’a na bakin cikin a rannan sai ya dauka majusawa iraniyawa yan shi’a ke yi ko kuma a ce kayi bata ka zama zindiki. Shi Yazid dinnan wanda ma’abucin Ruhul Bayan ya tsinewa kafin shi Manzon Allah ya tsine masa a Sahihul Bukhari da sauran littafan Sunnah,a Sahihul Bukhari na Al-imam Abu Abdillah Muhammad bin Isma’il bin Ibrahim bin Bardizagiye( saboda shi bafarise ne wato shi ma kakanninsa majusawa ne?)Al-ju’ufi(zamu yi magana nan gaba akan me ake nufi da AL-JU’UFI),cikakken sunan littafin shine Al-jami’u Al-musnad Al-sahihul mukhtasar(ku rike kalmar MUKHTASAR za mu yi magana akanta nan gaba saboda ku gane littafin gajeren littafi ne) wannan sunan littafin kenan na asali amma mutane basa karanta shi har karshe.To a cikin wannan littafin ne a kitabul Fitan a Babu Qaulin Nabiy halaku ummatiy ala yadiy Ugailama Sufaha daga Manzon Allah(saw) da isnadin day a tuke zuwa kakan rawin cewa KUNTU JALISAN MA’A ABI HURAIRA ma’ana na kasance tare da Abi Huraira wato shi kakan rawin a masallacin Annabi a Madina alhali a tare da mu akwai Marwan bn Hakam sai Abu huraira yace na ji Sadiqal masduq na cewa HALAKATU UMMATIY ALA YADAY GILMATUN MIN KURAISH ma’ana Halakan al’ummata zata kasance ne a hannayen wasu yara daga Khuraishawa sai Maryan yace:LA’ANATULLAHI ALAIHIM GILMATUN GILMA ma’ana La’anan Allah ta tabbata a gare su kananan yara,sai Abu huraira yace da na so in ce yayan gidan wane da wane da na fadi,sai na kasance(wato wanda ya rawaito riwayan) ina fita tare da kaka na zuwa ga Banu marwan(wato Banu umayyah) a lokacin da suke mulki a Sham,to a lokacin idan kaka na ya gansu kananan yara ne samari sai yace mana ina ga wadannan sune wadanda Annabi yace halaka al’umma ta na hannayensu mu kuma sai mu ce kai kafi kowa sani. Ibn Hajr Asqalani a sharhin Fathul bari yayi sharhin hadisin a juz’I na 17 shafi 18,Kitabul Fitan Bab Qaulin nabiy halaku ummatiy ala yadayi ugailama sufaha ya rawaito cewa Abu Huraira ya kasance yana tafiya a kasuwan madina yana cikin tashin hankali yana cewa ALLAHUMMA LA TADRIKNI SANATA SITTIN WALA IMARATAN SIBYAN wato Ya Allah kada ka riskar dani shekara sittin bayan hijra kuma kada ka riskar dani shugabancin yara,wadannan sune su Yazid wanda ya zama shugaba a shekara sittin bayan hijra yana kamar shekara talatin da takwas saboda haka idan ka ji wani na cewa Yazid Radiyallahu anhu bai san wadannan bayanan ba ko kuma ya sani amma kamar yanda Alusi ke cewa irin wannan dan kungiyar siyasar Yazid ne kamar yanda muke alfari cewa mu shi’an Ali ne,ka ga ya kamata irin wannan mutumin yayi saraha ya fadi shi dan shi’an Yazid ko shi’atu Abi sufyan ne.Me yasa irin wannan mutumin da baiyi imani da takiyya yake yi ba?idan yace sunna ba yana nufin sunna annabi bane ya na nufin Yazid ne,sannan ba takiyya sunan ta ba sunan ta nifaq da yaudara domin takiyya ba munafurci bane,Takiyya boye gaskiya ne da bayyana akasinta amma munafunci kuwa boye karya ne da bayyana gaskiya sun bambamta a asali.Takiyya asalinta gaskiya kamar yanda ya zo kur’ani ILLA MAN UKRIHA WA QALBUHU MUDMA’INNUN BIL IMAN wato sai wanda a tilasta mai alhali zuciyarsa tana cike da natse da imani,wannan shine takiyyah amma Nifaq kuwa shine boye karya da bayyana gaskiya kamar yanda Allah ke cewa KULLAMA AUKADU NARAN LIL HARBI ADFA’AHALLAH WA YAS’AUNA FIL ARDI FASADAN WALLAHU LA YUHIBBUL MUFSIDIN wato Duk lokacin da suka hasa wuta ta yaki sai Allah ya kasha wutan kuma suna sa’ayi domin barna a cikin kasa kuma Allah baya son mabarnata. Dawo wa ga littafin Fathul Bari cewa Abu Huraira na rokon Allah a kasuwan madina kada Allah ya riskar da shi shekara sittin bayan hijra da kuma mulkin kananan yara.Sai Ibn Hajar ya cigaba yana cewa to a cikin wannan al’amarin ta bayyana cewa wadannan samarin su fara mulki a shekara sittin ne,to waye wannan wanda ya fara mulki a shekara sittin?shine Yazid in ji Ibn Hajar domin haka al’amarin ya faru saboda Yazid dan Mu’awiya a wannan shekaran aka kalifantar dashi,ya cigaba da shuganci har shekara ta sittin da hudu ya mutu sannan sai aka kalifantar dan Yazid din wato Mu’awiya.shi wannan Mu’awiya dan Yazid din kwana arba’in kawai yayi yace wannan ba al’amarin mu bane saboda haka ga kayanku ya kuma ya boye a cikin gida ba a gara ganinshi har sai saida ya rasu.Ibn Hajar ya cigaba da cewa Yazid ne na farkon wadannan kananan yaran kamar yanda Abu huraira yayi nuni akanshi sai yace Fadakarwa:-Akwai ban mamaki da Abu huraira ya bada labarin wadannan yaran sai Marwan ya tsinewa masu saboda yaran yayansa ne a zahiri,tana iya yiwu wa Allah ne ya gudanar da tsinuwar akan harshen Marwan domin hujja tafi tsanani akansu kila su wa’azattu. Wannan ke nuna maka cewa bamu tafi akan dukkan hadisan Bukhari ba daidai bane kamar yanda yake bamu tafi akan dukkan hadisan daidai ne,mu bamu yi kama wanda yace duk wanda yayi amfani hadisan Bukhari ya zama zindiki daga cikin malaman sunna sannan ba mu zama wanda yace dukkan hadisan Bukhari ingattattu ne.Abinda muke cewa shine duk abinda Bukhari ya kebanta dashi shi kadai a duniya bamu yarda dashi ko kuma ya sabawa shari’a in banda haka akwai shiriya a cikinsa mai yawa288
28 Yuni 2015 - 13:32
Lambar labari: 697823
Daga Shaikh Hamzah Muhammad Lawal MANZON ALLAH YA TSINEWA YAZID YA KUMA YI BAYANIN KASHEN IMAM HUSAIN TARE DA KUKA KAFIN KASHE SHI A KARBALA