Kungiyar Taliban ta ce ita ce ta kai harin, inda ta rika tashin bama-bamai da rokoki da gurneti-gurneti a ciki da wajen majalisar.
'Yan bindigar dai sun yi yukurin kutsa kai cikin majalisar dokokin, koda yake ba su yi nasara ba.
Kakakin ma'aikatar cikin gida ta kasar ya ce babu dan majalisar da ya samu rauni, sai dai kimanin mutane 20 sun ji rauni sakamakon fashewar da gilasai suka yi.
Ma'aikatar lafiya ta ce babu wanda ke cikin mummunan yanayi a cikin mutanen da suka ji rauni.
An kai harin ne a lokacin da majalisar ke zama domin nada sabon ministan tsaron kasar.288