6 Yuni 2015 - 10:45

Hukumomi a kasar Mali da 'yan tawayen Abzinawan kasar sun ratafa hannu kan wata yarjejeniya da ta bukaci a tsagaita wuta a tsakaninsu.

Hakan dai ya bada dama wajen cimma yarjejeniyar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta Cimawa  na kokarin ganin an samu  kawo karshen yakin da suka dauki  tsahon shekaru suna tafkawa  da juna a arewacin kasar. Babban  wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Malin Mongi Hamdi ne ya bayyana  hakan inda ya ce daya daga cikin matakan yarjejeniyar ya bukaci da a tsagaita wuta a garin Menaka da ke arewacin kasar  da kuma janyewar mayakan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin ta Mali a yankin, inda ya ce za a maye gurbinsu da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani lokaci. Su dai 'yan tawayen Malin na fafutukar samar da 'yancin kan yankin Abzinawa ne wanda suka yiwa lakabi da Azawad.ABNA