Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa tace bayan idar da Sallar Magariba a jiya Alhamis dan kunar bakin wake ya tayar da bom a kasuwar Fallujah a Jimeta.
Wannan na zuwa ne bayan an kai wani harin Bom a garin Maiduguri a jiya Alhamis inda wata budaddiyar mota da abkawa wani shingen bincike a kusa da barikin Sojoji.
Jerin hare haren na zuwa a yayin da sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kammala ziyara a kasashen Nijar da Chadi kan yadda za a kawo karshen mayakan Boko Haram da ke addabar yankin arewa maso gabaci da kuma kasashen da ke kewaye da tabkin Chadi.ABNA