A cewarta, faduwar farashin man fetur a duniya ya sanya tun daga watan Janairun bana zuwa yanzu, gwamnati ta ci bashin fiye da naira biliyan 400.
Iweala ta ce, "Daga cikin naira biliyan 882 da aka amince a karbo bashi a cikin kasafin kudin bana, a yanzu haka gwamnati ta ci bashin naira biliyan 473 domin gudanar da ayyuka da kuma biyan albashi."
Wannan labarin ba zai yi wa gwamnatin Janar Muhammadu Buhari wacce za ta karba mulki a ranar 29 ga watan Mayu ba, saboda kasancewa zai soma mulki ne a lokacin da tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal.
Masu sharhi na ganin cewar matsalar tattalin arzikin na da nasaba da irin makudan kudaden da aka kashe lokacin zaben da aka gudanar a kasar a 'yan makonnin da suka wuce.ABNA