11 Mayu 2025 - 22:56
Source: Irna
Isra'ila Na Ci Gaba Da Ruwan Bama-Bamai A Tashishin Jiragen Ruwan Yemen

Majiyoyin labarai sun rawaito cewa jiragen yakin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a tashar jiragen ruwa na lardin Hodeidah na kasar Yaman.

A cewar rahoton da IRNA ta fitar an fara wadannan hare-haren ne mintuna kadan da suka wuce kuma har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare.

A baya dai sojojin Isra'ila sun sanar a cikin wani sako da suka aike wa mutanen da ke tashar jiragen ruwa na Hodeidah, Salif da Ras Issa da su gaggauta ficewa daga wadannan tashohin domin kare lafiyarsu.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi ikirarin cewa kungiyar Ansarullah na amfani da wadannan tashoshin jiragen ruwa wajen yin ayyukan ta'addancinsu.

Gwamnatin Isra'ila ta yi gargadin ficewa daga tashoshin jiragen ruwa na kasar Yemen guda uku

Gwamnatin Isra'ila ta gargadi ma'aikatan tashoshin jiragen ruwa uku na kasar Yemen da su gaggauta barin wadannan tashoshin jiragen ruwa.

Tashar talabijin ta Al-Aqsa cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar a cikin wani sako da ta aike wa mutanen da ke tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Salif da kuma Ras Issa da su gaggauta ficewa daga wadannan tashoshin jiragen ruwa domin kare lafiyarsu.

Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi ikirarin cewa kungiyar Ansarullah na amfani da wadannan tashoshin jiragen ruwa ne wajen ayyukansu na hare-haren da su ke kaiwa Isra'ila.

Kasar Yemen ta kasance tana taka muhimmiyar rawa a ci gaban tsaro a yankin a cikin 'yan watannin da suka gabata tare da karuwar hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan wuraren da makiya yahudawan sahyoniya suke a matsayin mayar da martani ga kawanya da wuce gona da iri.

Amurka tare da goyon bayan gwamnatin yahudawan sahyoniya da kuma kokarin karya kawanya da sojojin ruwan kasar Yemen suka yiwa gwamnatin kasar, tana ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula na kasar Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar samun shahidai da dama.

Duk da wadannan hare-hare, sojojin kasar Yemen na ci gaba da goyon bayan gwagwarmaya da al'ummar Palastinu a zirin Gaza, tare da gudanar da ayyuka na musamman, sun auna tsakiyar yankunan da aka mamaye, da kai hari kan jiragen ruwa masu alaka da gwamnatin sahyoniyawa, da ma na Amurka a tekun Bahar Maliya da Tekun Indiya, tare da harbo jiragen sama marasa matuka na Amurka da dama.

Your Comment

You are replying to: .
captcha