7 Mayu 2025 - 10:56
Source: ABNA24
Lebnon: Isra’ila Ta Kai Hari Kan Wata Mota Mutun Daya Yayi Shahada

Mamaya na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Lebanon daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar kai hare-hare tare da kashe 'yan kasar ba tare da hukuma ta dauki wani mataki ba.

Wani dan kasar Lebanon ya yi shahad a safiyar yau Laraba lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wata mota a birnin Sidon da ke kudancin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: wani jirgin sama mara matuki na makiya Isra'ila ya kai hari kan wata mota mai mai tafiya a unguwar Villa da ke kusa da masallacin Imam Ali a birnin Sidon, lamarin da ya yi sanadiyara shahadar mutum guda.

Mamaya na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Lebanon daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar kai hare-hare tare da kashe 'yan kasar ba tare da hukuma ta dauki wani mataki ba.

A ranar 8 ga Oktoba, 2023, mamayar ta kaddamar da farmaki kan kasar Labanon, wanda ya rikide zuwa yakin da aka yi a ranar 23 ga Satumba, 2024, wanda ya yi sanadin shahidai sama da 4,000, kimanin 17,000 suka samu raunuka, da kuma raba kusan mutane miliyan 1.4 daga wuraren su.

Your Comment

You are replying to: .
captcha