Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a farkon jawabinsa, Jagoran juyin juya halin Musulunci, yayin da ya karbi bakuncin jami’an aikin Hajji a yau Lahadi, ya yi ishara da wannan mummunan lamari da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee da ke yankin Bandar Abbas a kudancin kasar, inda ya mika ta’aziyya da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da wadanda suka jikkata a lamarin.
Jagoran ya ce, “Hakika wannan lamari ne mai daci da ban tausayi a gare mu baki daya, iyalan wadanda abin ya shafa sun rasa ‘yan uwansu, muna jajanta musu da cewa idan muka yi hakuri a kan matsalolin rayuwa daban-daban, ladan da Allah Madaukakin Sarki zai ba mu kan wannan hakurin zai ninka har sau dubbai da daraja fiye da dacin wannan bala’in.
"أولئك عليهم صلوات من ربهم" -
“Waɗannan albarka ta tabbata agare su daga Ubangijinsu” – waɗanda suka yi haƙuri, Allah Ya lulluɓe su da rahamarsa. Wannan yana da matukar muhimmanci. In shaa Allahu zai sanyaya zukatansu ya sanya masu nutsuwa da kwanciyar hankali.
Jagoran ya jaddada dangane da lamarin Hajji: Hajji farilla ne—watakila a iya cewa shi kadai ne wajibci— wanda siffarsa da tsarinsa na waje ya zamo na siyasa dari bisa dari. Wannan wajibcin yana tara mutane wuri guda, a lokaci guda, kowace shekara, tare da hada duk wanda zai iya aiwatarwa. To menene wannan? Haɗuwar jama'a, tara jama'a tare, ainihin wannan aiki yana da yanayin siyasa. Don haka Hajji sabanin kokari da maganganu da ayyukan wasu masu gurbata wannan gaskiya yana da dabi’a ta siyasa, kuma siffarsa da tsarinsa ma na siyasa ne.
Daga nan sai Ayatullah Khamenei ya sake duba wani bangare na tafsirin ayar ta
"ليشهدوا منافع لهم"
"domin su shaida Abubuwan masu anfanarwa ga kawukansu," yana mai cewa: Taron aikin Hajji na amfanir bil'adama ne, kuma babu wata maslaha ga al'ummar musulmi da ta wuce maslahar hadin kai. Da a ce al'umma ta kasance a hade, da bala'in Palastinu da Gaza ba zai faru ba, da kuma Yemen din ba za ta fuskanci matsin lamba irin wannan ba.
Your Comment