Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau ne aka gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na "masu yaɗa labaran Ahlulbaiti (AS)" bisa munasabar kwanaki goma na karama tare da halartar masu fafutuka da masana daga Iran da nahiyar Afirka tare da ɗaukar nauyin kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) - ABNA, a zauren majalissar Ahlul-bayt (AS).
Aci gaba da taron; Ayatullah Ramezani ya ci gaba da cewa: A yau jihadi a fagen yada labarai da na intanet bai gaza jihadi a zahiri ba. Duk wadanda suke nan suna yin jihadi ne kuma muna fatan mu shaida al'amura masu kyau tare da masu ƴada labari a cikin kasashensu. Muna da wadatar batutuwan da zamu fitar kuma ya kamata a nuna wannan wadatar batutuwan da kyau a sararin samaniya.
Babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kammala da cewa: A fagen fasahar na'urar wuce gadi ma, wajibi ne mu kai ga matakin samar da abubuwan da muke da bukata. Babu wani batu mai kyau kamar na Ahlul Baiti a duniya. Idan muka gabatar da wannan batun cikin a cikin tsari masu kyau da inganci a cikin sararin samaniya, za mu iya yin nasara a wannan fagen. Idan aka yi la’akari da siffofi kebantattu na wayewar Musulunci, za mu iya cinye fagagen tunani a fagagen duniya. Don haka ya kamata cibiyoyi irin su cibiyar sadarwar intanet ta kasa su kara daukar matakai a fagen samar da wani dandali na abubuwan da suka shafi addini da na Musulunci cikin kyakkayawan yanayi kuma masu dacewa. Wajibi ne mu gabatar da addinin Musulunci gaba daya kuma daidai yadda ya ke, ba gurbatattun Musulunci da ake yada shi a kasashen Yamma ba. Musuluncin Ahlul Baiti ya sha bamban da Musuluncin da aka yadawa a kasashen Yamma. A kasashen yamma, wasu na neman kawarwa da shigar Musulunci cikin al'adun Turawa, amma dole ne mu gabatar da Musulunci gaba dayansa da ingancinsa.
Your Comment