17 Disamba 2025 - 21:58
Source: ABNA24
Yadda Aka Gudanar Da Taron Mauludin Sayyidah Zahra As Katsina + Hotuna

Wasu daga cikin hotunan yadda taron Mauludin Sayyida Fatima (S.A) wanda 'yan uwa na da'irar Katsina suka gabatar a ranar Litinin 24/Jimada Thani, dai dai da 15/Disamba/2025, a muhallin Markaz.

Babban bakon da ya gabatar da jawabi a wajen taron shi ne, Sheikh Muhammad Darul Hikima ɗan asalin jihar Katsina, mazaunin ƙasar Ghana. Inda ya bayyana matsayin Sayyida Fatima (S.A), da kuma wajabcin da ya hau kan kowane mutum na so da kuma biyayya a gare ta.

Daga karshe Sheikh Yakub Yahya Katsina ya rufe taron da addu'a, bayan gabatar da kyautar littafai da Sheikh Muhammad Darul Hikima ya ba masu suna Fatima. Sannan kuma ya ba Sheikh Yakub na shi kyautar littatafan. 

17/12/2025.

Your Comment

You are replying to: .
captcha