27 Afirilu 2025 - 09:27
Source: ABNA24
Hamas Ta Tattauna Da Masu Shiga Tsakani A Birnin Alkahira Kan Batun Tsagaita Wuta

Taron ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na kai agaji da kayayyaki ga al'ummar yankin.

Tawagar shugabannin Hamas karkashin jagorancin Mohammed Darwish, shugaban majalisar gudanarwar kungiyar, tare da sauran 'yan majalisar, ta bar birnin Alkahira da yammacin ranar Asabar bayan tattaunawa da shawarwari da mahukuntan Masar. Tattaunawar ta shafi kokarin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin da ake yi da al'ummar Palastinu a zirin Gaza, da kuma dukkan batutuwan da suka shafi hakan.

Tawagar ta sake duba manufar kungiyar na cimma cikakkiyar yarjejeniya da za ta hada da tsagaita wuta, musayar fursunoni, agaji, da sake gina kasar. An amince da kara yin kokari tare da ci gaba da sadarwa don tabbatar da nasarar wadannan kokarin.

Tawagar shugabannin Hamas ta isa birnin Alkahira domin tattaunawa kan manufar kungiyar na tsagaita wuta da musayar fursunoni.

An kuma yi tir da halin da ake ciki na rashin jin kai a zirin Gaza, bayan watanni biyu da aka shafe ana tsaurara matakan tsaro da kuma hana shigar da kayan agaji da abinci da magunguna da yan mamaya suka yi a yankin. Taron ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na kai agaji da kayayyaki ga al'ummar yankin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha