Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (As) -Abna- ya habarto maku cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da wata sanarwa a hukumance tana musanta alaka da harin makami mai linzami da aka kai yau daga kasar Lebanon zuwa yankunan arewacin kasar Falasɗinun da Isra'ila ta mamaye.
A nata bayanin kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa tana nan a kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Tana mai cewa: Ba mu da alaka da harin makami mai linzami da aka kai a arewacin Falasdinu. tana mai jaddada cewa ikrarin tuhumar makiya Isra'ila wani neman uzuri ne kawai da suka fake d shi na ci gaba da kai hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan kasar Labanon, wanda tun bayan sanar da tsagaita bude wuta a kasar Lebanon ba ta daina ba.
Kungiyar Hizbullah ta jaddada kudurinta na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma goyon bayan gwamnatin kasar Labanon wajen tinkarar wannan mummunan tashin hankali da yahudawan sahyuniya suke yi kan kasar Labanon.
Nabih Berri a nasa martanin: Tel Aviv ta fi amfanar ci gaba da kai hare-haren sama da kasar Labanon a cikin yaki Shugaban Majalisar Dokokin Labanon: Ɓangaren da ya fi cin gajiyar jefa Lebanon da yankin cikin rikici ita ce gwamnatin Sahayoniya.
Muna kira ga sojojin Lebanon da hukumomin shari'a da na tsaro da su gudanar da bincike kan abin da ya faru a safiyar yau a kudancin Lebanon.
A safiyar yau din dai ne Isra'ila ta kai hari a Kudancin Labanon inda Mutane 4 ne suka yi shahada yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kaia garin "Tulin" da ke kudancin kasar Labanon Kafofin yada labarai a kasar Labanon na cewa an samu karuwar shahidai a garin Tolin da ke kudancin kasar ta Lebanon sakamakon hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a yammacin yau. Don haka adadin shahidan wannan hari ya karu zuwa mutane 4.
Kawo yanzu dai an bayyana adadin wadanda suka jikkata zuwa 10, yayin da daya daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.
Your Comment