6 Nuwamba 2025 - 15:58
Source: ABNA24
Yaduwar ‘Yan Ta’addan Al-Qaeda A Afirka Tun Daga Mali Zuwa Najeriya

Ƙungiyar Nusratul-Islam wal-Muslimeen - reshen al-Qaeda a Sahel - an kafa ta ne daga rassan cikin gida da dama a Mali, kuma a yau, ta hanyar hauhawar tashin hankali da shugabanci mai kama da juna, ta zama ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka fi tasiri a yankin.

Ƙungiyar Nusratul-Islam wal-Muslimeen reshen al-Qaeda a yankin Sahel wanda aka kafa a watan Maris na 2017 bayan haɗakar ƙungiyoyi da dama da ke aiki a Mali, ciki har da Ansarud-Din da Rundunar Masina. Kungiyar tana amfani da wata hanya ta haɗaka wadda ke bayyane a cikin ayyukan makamai da kuma bayyana manufofin gudanar da mulki na cikin gida. Kafa kotunan Shari'a na gida, sanya haraji da kuma tara harajin hanya suna daga cikin kayan aikin da ke ba ta damar kafa kasancewarta a yankunan karkara ba tare da kasancewar gwamnati ba. Ƙasashen Turai sun sanya wannan ƙungiyar a cikin jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugabanni da Tsarinsu:

Iyad Agh Ghali ne ke jagorantar ƙungiyar, wani babban mutum daga ƙabilar Tuareg a arewacin Mali. Daga cikin fitattun abokan aikinsa masu leƙen asiri akwai Amadou Kafa, kwamandan Rundunar Masina a tsakiyar ƙasar. Dukansu suna ƙarƙashin takunkumin Majalisar Dinkin Duniya. A watan Yunin 2024, Kotun Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Iyad bisa laifin take haƙƙin ɗan adam a lokacin da ƙungiyoyin masu dauke da makamai ke iko da Timbuktu (2012–2013), wanda hakan ke nuna sauyin ƙungiyar daga tawayen cikin gida zuwa ayyukanta a yanki a yanzu.

Girman Kungiyar Da Ƙarfin Yaƙi Da Da’awa:

Rahotanni da aka samu daga majiyoyin da ba a bayyana ba ya nuna cewa ƙungiyar tana da mayaka dubbai. Rahotanni da nazarin da aka samu a fagen daga sun gano ƙungiyar a matsayin rundunar yaƙi mafi inganci a yankin Sahel; a wasu yankuna na Mali da Burkina Faso, ƙarfinta ya zarce na ƙungiyoyi masu hamayya da ma dakarun gwamnati. Misalin ƙarfin yaƙinta shine mummunan harin da aka kai a watan Afrilun 2025 a Benin, wanda gwamnatin Benin ta ba da rahoton mutuwar sojoji 54 kuma ƙungiyar ta ɗauki alhakin hakan.

Shin Bamako Na Cikin Haɗarin Faɗuwa Kuwa?

Duk da cewa hari kai tsaye a Bamako a dan knanin lokaci da alama ba zai yiwu ba, amma ƙungiyar ta nuna cewa za ta iya kewaye babban birnin ta hanyoyi da ba’a tsammata ba. Tun daga watan Satumba, an kai hari kan ayarin motocin mai da aka shigo da su daga Senegal kuma an cin wuta ga da dama daga cikin tankunan mai kusa da Kayes, wanda ya haifar da ƙarancin mai a Bamako. A ƙarshen Oktoba, gwamnati ta tilasta rufe makarantu da jami'o'i, rage yawan amfani da mai, da kuma dogayen layukan mai da aka kafa a gidajen mai. Manufar waɗannan dabarun shine a gurgunta rayuwar yau da kullun, da rage amincewa da gwamnati, da kuma tilasta mata ja da baya; barazanar wanzuwa wadda ba lallai bane ta buƙaci kai hari kai tsaye ba.

Faɗaɗa iyakokin Al-Qaeda a Afirka/daga Mali zuwa Najeriya

Ayyukan ƙungiyar sun fi mayar da hankali ne a Mali da Burkina Faso, kuma tana ci gaba da aiki a kudu maso yammacin Nijar. Tun daga shekarar 2022, ta faɗaɗa arewa zuwa Benin, kuma motsin binciken ta yaɗu har zuwa Togo da Ivory Coast. Sanarwar da aka fitar kwanan nan game da wani aiki a Najeriya ta nuna ƙaruwar tasirin ƙungiyar a kan iyakokinta da kuma cin zarafin iyakokinta marasa kariya. A martanin da ta mayar, ƙasashe sun ƙara ƙarfin kula da kan iyakoki da kuma ƙara sintiri a wuraren shakatawa da wuraren da aka killace.

Dabarun Yaƙi:

Ƙungiyar ta nuna babban matakin karfinta tun daga kwanton bauna masu sarkakiya da hare-haren sansani zuwa dasa bama-bamai a gefen hanya. A gefe guda kuma, tana aiwatar da aikin shugabanci kamar tattara zakka daga 'yan kasuwa da manoma, takaita zirga-zirga, da kuma sarrafa hanyoyi. A wannan shekarar, ta ƙara ƙarfin kayan aikin tattalin arzikinta tare da iyakance mai wanda ya sanya hauhawar farashin kudaden ilimi, sufuri, da abinci. Ƙungiyar tana kuma amfani da kayan aikin kasuwanci da na fasaha: aika saƙonni, ƙananan jiragen leƙen asiri marasa matuƙa, har ma da intanet ta tauraron ɗan adam lokacin da hanyoyin sadarwa na wayar hannu suka lalace. Duk da cewa ba a san takamaiman adadin da ke amfani da kayan aikin ba, saurin amfani da fasahar a bayyane yake a tsakanin ƙungiyoyin masu dauke da makamai na Sahel.

Hanyoyin Da Suke Samun Kuɗaɗe:

Ƙungiyar ta dogara ne akan hanyoyin samun duki na cikin gida, ciki har da kuɗin harajin shigar da kayayyaki, kudaden fansa daga garkuwa da mutane, satar shanu, samun kaso da riba daga haƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba. Cibiyoyin safarar kuɗi na ƙetaren iyaka da tsarin aika kuɗi ba bisa ƙa'ida na (hawala da makamantansu) suke kulawa da harkar kuɗi ko da a ƙarƙashin takunkumi. Waɗannan hanyoyin suna ba ƙungiyar sassauci da juriya fiye da ƙungiyoyi masu kuɗaɗen shiga masu tsari.

Dangantaka Da Ƙungiyoyin ISIS:

Ƙungiyar tana cikin gasa koyaushe da ƙungiyoyin ISIS a Sahel da Yammacin Afirka; a fannoni masu tasiri, gasa don ɗaukar ma'aikata, sarrafa albarkatu, da hanyoyin sufuri tsakanin ɓangarorin suna ƙaruwa. A wasu yankuna, lamurorinsu suna gudanar da su a keɓe ba sa haɗaka da wasu kungiyoyin. Yin aikin wasu al'ummomin yankin tare da ƙungiyar wani lokacin yana faruwa ne ta hanyar matsin lamba ko kuma don biyan bukatunsu da suka hadu akai; A yankunan da babu gwamnati ko kuma ake ganin ba a maraba da su suna daukarsu (a matsayin gungun yan kore), ƙungiyoyi suna cike gurbi ta hanyar kafa gwamnatoci masu kama da juna da kuma bayar da mafitae cikin gida, suna sanya tsarin da suke so ta hanyar tilastawa da tsoratarwa, ta haka ne za su iya ɗaukar ma'aikata, musamman daga matasa marasa galihu. Wannan dabarar ci gaba ce ta hanyar da al-Qaeda ke bi a hankali wajen shiga cikin al'umma.

Sauyi Na Baya-Bayan Nan Da Suke Faruwa A Najeriya:

A ranar 28 ga Oktoba, 2025, ƙungiyar ta sanar da harinta na farko a cikin Najeriya, tana iƙirarin kashe wani soja a Jihar Kwara (kusa da kan iyaka da Benin). Najeriya ta riga ta fuskanci barazana daga Boko Haram wani reshen ISIS; shigar wani bangaren na uku da ke da alaƙa da al-Qaeda kuma gogaggen a ayyukan ƙetaren iyaka na iya haifar da ƙirƙirar sabbin shafukan rikici a kan iyakokin kan iyaka da hanyoyin fasa-kwauri tsakanin Benin, Nijar, da Najeriya. Wannan sanarwar ta nuna manyan fannoni biyu na dabaru: na farko shine damar da ƙungiyar ke da ita wajen amfani da gibin tsaron kan iyaka da yankunan da ba su da kyau, na biyu kuma shine saƙonta ga magoya baya da abokan hamayya game da isa gare ta. Ko ƙungiyar za ta iya kafa zama na dindindin a Najeriya ya dogara ne da abubuwan da suka shafi dabaru, samuwar mafaka a Benin da Nijar, da kuma ƙarfin dakarun yankin da ba su da ƙarfi a Najeriya.

Yunkurin Gwamnati:

Najeriya ta karɓi tallafin ƙasashen waje amma ta dage kan kiyaye ikonta. Benin ta ƙarfafa haɗin gwiwa a yankin bayan hare-haren a watan Afrilu. Mali ta kuma nemi wasu hanyoyin samar da mai, ana kyautata zaton ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Rasha don samar da mai, kuma tana ƙoƙarin karya shingen ta hanyar samar da rakiyar sojoji ga ayarin motoci. Duk da haka, waɗannan martanin galibi na ɗan lokaci ne kuma ba sa magance tushen matsalar - raunin shugabancin gida - wani abu ne da ƙungiyar ke amfani da shi.

Abubuwan Da Ake Sa Ran Su Nan Gaba:

Ganin halin da ake ciki a yanzu, akwai yiwuwar ƙaruwa, gami da ci gaba da dabarun toshe hanyoyin Bamako ta hanyar kai hari kan ayarin motoci da toshe mai da hatsi a kusa da Kais da hanyar Senegal, da kuma haɗarin ƙara kutsawa cikin Togo da Ghana. Rahotannin jiragen sama marasa matuƙa da kayan aikin sadarwa na tauraron ɗan adam da aka kwace daga rundunonin da ke da alaƙa da ƙungiyar sun nuna cewa ƙarfin fiagensu yana canzawa. Kowace sanarwa da Iyad Ag Ghali ko Amadou Kafa suka yi game da Najeriya ko biranen Sahel da kanta yana nuna niyyarsu fiye da saninta da kuma shirye-shiryen ƙarfafa tasirin yankin.

A takaice dai, ƙungiyar Nusratul-Islam wa al-Muslimeen (NUS) ta rikide daga ƙungiyar 'yan tawaye ta gida a Mali zuwa ƙungiyar da ke amfani da matsin tattalin arziki da kuma tsarin gwamnati mai kama da juna. Sanarwar wani hari a Najeriya ba ta da wani tasiri a fannin tattalin arziki, amma tasirin dabarunta da kuma tasirinsu sun wuce haka; wannan misali ya nuna cewa iyakoki ba su da wani shinge ga waɗannan ƙungiyoyi kuma yankin Sahel yana gab da shiga wani yanayi na rashin kwanciyar hankali a kan iyakoki. A Bamako, tambayar ba ita ce ko za su mamaye babban birnin ba, a’a sai ko za su mamaye ta a hankali maimakon kai hari kai tsaye. — Kuma amsar yanzu ita ce: Wannan aikin yana ci gaba.

................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha