Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hari Ta Sama Da Kasa A Kudancin Lebanon.

Wajibi Ne Hukumar Labanon Ta Sake Sabon Lale Dangane Da Siyasar Tsaronta
7 Nuwamba 2025 - 16:51
Source: ABNA24
Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hari Ta Sama Da Kasa A Kudancin Lebanon.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare kan garuruwa da dama a kudancin Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare guda biyu a garuruwan Tayr Dibba da Aita al-Jabal a ranar Alhamis, sannan suka kai hari kan wani gida a garin Taybeh, a kudancin Lebanon.

A cikin wannan yanayi, ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ba da rahoton cewa mutum ɗaya ya ji rauni sakamakon harin da Isra'ila ta kai wa garin Tayr Dibba.

A wani labarin kuma, jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari kan garin Zawtar al-Sharqiyah a gundumar Nabatieh, sannan suka kai hari kan wani gini a garin Kfardounine a gundumar Bint Jbeil, a kudancin ƙasar.

A wani yanayi makamancin haka, wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa sojojin mamaye sun harba harsasai masu linzami daga wurin "Miskav Am" zuwa garuruwan Lebanon da ke makwabtaka, yana mai kara da cewa jiragen sama marasa matuki na abokan gaba suna ci gaba da shawagi a wurare da dama a kudancin.

Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta sanar a jiya, Alhamis cewa mutum daya ya mutu wasu uku kuma sun jikkata a wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wani injin katako a Tyre.

A safiyar yau, jiragen saman Isra'ila sun kai hari kan yankin Sharafiyat da ke wajen garin Abbasiya, a kudancin Lebanon.

A wani hari kuma, wani jirgin sama mai saukar ungulu na Isra'ila ya jefa bam mai ban tsoro a yankin Ras al-Naqoura.

Hare-hare ba kakkautawa harzuwa loakcin watsa wannan rahaton tare da yin shurin shugabannin Labanon.

.................

Your Comment

You are replying to: .
captcha