Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Hussein Al-Hajj Hassan, memba na kungiyar Hizbullah a majalisar Lebanon, a wata hira da ya yi da shirin "Almasa’iyyah" na Al-Jazeera ya sanar da cewa Hizbullah ta gargadi manyan jami'ai uku a kasar da kuma al'ummar Lebanon kan kokarin Amurka da gwamnatin mamaya na jawo Lebanon cikin tarkon siyasa da diflomasiyya.
Ya bayyana cewa wasikar ta kunshi manyan sassa biyu; na farko, tana da alaka da yarjejeniyar da aka kammala a shekarar 2024 wacce Amurka da Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka shiga tsakani, kuma Lebanon ta zartar da dukkan sassan wnanan yarjejeniya, amma gwamnatin Isra’ila tare da goyon bayan Amurka a fili, ta ci gaba da kai hare-hare da rusawa da lalatawa tare da kashe-kashe.
Hajj Hassan ya ƙara da cewa: Washington ta wuce gona da iri kan iyakokin kudurin Majalisar Tsaro mai lamba 1701 da yarjejeniyar 17 ga Nuwamba, 2014 a cikin ayyukanta kuma ta karya abin da ake kira "tsarin Makansim" da ake gudanarwa ƙarƙashin kulawar wani jami'in Amurka.
Ya jaddada cewa Hizbullah ta yi kira ga gwamnati da ta matsa wa Amurka, Faransa, da Majalisar Dinkin Duniya lamba don su ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da kuma ɗaukar matsayi ɗaya tilo mai inganci.
A bangare na biyu na wasiƙar, Hizbullah ta yi gargaɗin cewa shawarar tattaunawa da Isra’ala da Amurka ta bayar ta gabatar da ita ne cikin kakkausar murya da ba ladabin diflomasiyya a ciki, kuma burinsu shine tilasta ja da baya a jere ga Lebanon.
Da yake magana game da tarihin gwamnatin yahudawa na rashin bin yarjejeniyoyi, Hajj Hassan ya ce: Wannan gwamnatin koyaushe tana neman muradun gefe ɗaya kuma bai kamata ta faɗa cikin tarkon irin waɗannan tattaunawar ba.
Ƙaruwar Matsin Lamba Da Hare-Haren Sama Kan Lebanon
Ya kuma nuna dagewar Isra’ila da girman kan Amurka, yana cewa: Gwamnatin Lebanon kwanan nan ta yanke muhimman shawarwari guda biyu, amma ba ta sami amsa daga Washington ko Tel Aviv ba. Maimakon haka, matakin karar tsamarin hare-hare da baƙaƙen maganganu ga Lebanon ya ƙaru, kuma jami'an Amurka sun yi amfani da kalaman ɓatanci don bayyana Lebanon a matsayin "ƙasar da ta sha kaye".
Al-Hajj Hassan ya ƙara da cewa: "Ƙarin hare-haren sama da gwamnatin Isra’ila ta ke kaiwa a kudancin Lebanon kwanan nan ya faru ne a cikin tsarin matsin lamba daga Amurka da gwamnatin Isra’ila kan gwamnatin Lebanon, gwagwarmaya da al’umma domin tilasta wa ƙasar ta ja baya".
A ƙarshe, ya ƙi amsa tambayar ɗan jaridar game da matakan Hizbullah don mayar da martani ga waɗannan hare-haren.
Your Comment