Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Yemen ta sanar a wata sanarwa a yau Asabar cewa wani aikin tsaro mai matakai da dama ya kai ga kama wata cibiyar leƙen asiri.
Yemen ta ce wannan cibiyar tana da alaƙa da ɗakin ayyukan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin leƙen asiri na Amurka da Isra'ila da hukumar leƙen asiri ta Saudiyya. Wanda Hedikwatar cibiyar tana cikin yankin Saudiyya.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Yemen ta ce bayan leƙen asiri, na sa ido da kuma ayyukan bin diddigin lamarin, ta yi nasarar dakile shirye-shiryen abokan gaba, hanyoyin aiki na wakilan cin amana da ke da alaƙa da wannan cibiya da kuma hanyoyin sadarwarta.
Your Comment