Harkar Hamas: Muna maraba da shirin Masar na sake gina Gaza, wanda aka amince da shi a taron kolin kasashen Larabawa, kuma muna kira da a samar da dukkan kayayyakin da za a yi nasarar wanna aiki.
Muna jaddada bukatar tilasta wa makiya masu aikata laifuka aiwatar da alkawurran da suka dauka a cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da yin kira da a matsa lamba ga masu mamaya da su fara mataki na biyu na shawarwari da ciyar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta gaba.
Masar ta sanar da cewa sake gina Gaza zai dauki shekaru 4.5
Ministan Harkokin Wajen Masar: A kashi na farko na sake gina Gaza, za a gina rukunin gidaje na dindindin 200,000. Kashi na farko zai ci kusan dala miliyan 20 kuma zai dauki kimanin shekaru 2 da rabi.
Da yake bayyana cewa shirin na Masar ya hada da gina tashar jiragen ruwa da filin tashi da saukar jiragen sama a zirin Gaza, Abdel Ati ya ci gaba da cewa: Dole ne a samu kashi na biyu don aiwatar da shirin tsagaita bude wuta a Gaza, kuma dole ne Isra'ila ta cika alkawuranta.
Your Comment