6 Mayu 2025 - 18:28
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Harba Bama-Bamai A Filin Jirgin Saman Sana'a + Bidiyo

Rundunar sojin Isra'ila ta ce filin tashi da saukar jiragen saman ya daina aiki gaba daya, inda suka zargi Houthis da amfani da shi wajen safarar makamai.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: Isra’ila ta kai hari filin sauka da tashin jirgin sama na San’a yamen inda bisa wasu rohotannin filin jirgin sama an dakatar da tashar jirgin saman birnin Sana’a wannan yana faruwa ne a rana ta biyu na hare-haren wuce gona da irin da take kaiwa kasar Yemen. Kamar yadda kuma ta yi ruwan bama-bamai a wuraren tatar mai da wutar lantarki da masana'antar siminti.

Rundunar sojin Isra'ila bisa ridi ta ce wai filin tashi da saukar jiragen saman ya daina aiki gaba daya, inda suka zargi Houthis da amfani da shi wajen safarar makamai.

Jiragen yakin Isra'ila sun kuma kai hare-hare a yammacin yau Talata, da tashoshin samar da wutar lantarki da 'yan Houthis ke amfani da su da kuma masana'antar siminti na Amran, wadanda ake zargin suna amfani da su wajen gina ramukan kasa.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa sojojin sun yi ruwan bama-bamai a tashar jirgin fasinja, da jiragen farar hula, da kuma wuraren hidima a filin jirgin saman Sanaa.

Isra’ila Ta Kai Hari A Gurare 10

Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, an kai harin ne a wurare 10 a kasar Yemen, da suka hada da filin jirgin sama na Sanaa, da wuraren tatar mai, da kuma gidajen mai.

Da sanyin safiyar yau ne dai rundunar sojin Isra'ila ta yi gargadin yin gaggawar ficewa daga yankin filin tashi da saukar jiragen sama na Sanaa da ke karkashin ikon 'yan Houthi a shirye-shiryen kai hari. Wannan dai na zuwa ne a ci gaba da kai hare-hare ta sama kan kasar Yemen.

Sabon harin da aka kai a filin jirgin saman babban birnin kasar ya zo ne kwana guda bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Yemen tare da hadin gwiwar Amurka, wanda ta ce wani martani ne ga harin makami mai linzami da aka kai kan filin jirgin saman Ben Gurion a ranar Lahadi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha