Ayatullah Khamenei: Aikin makarantar hauza shi ne kafa tushen manyan layukan da suka shafi sabuwar wayewar Musulunci/Bayyana abubuwan da ake bukata na babbar makarantar hauza a cikin al'ummar musulmi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin sakon da ya aike wa taron kasa da kasa da aka gudanar a wajen bikin cika shekaru 100 da sake kafa makarantar hauza ta birnin Qum, ya jaddada cewa: Babban aikin wannan makarantar shi ne "Bayyana Sakon Gaskiya", mafi kyawun misalai a cikinsu shi ne zayyana manya da kanana daga cikin wayewar Musulunci na zamani da gina al'umma, da yin bayani dalla-dalla ga al’adun musulunci.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA – ya kawo maku cikakken bayanin jagoran juyin jya halin musulunci, a cikin wani sakon da ya aike wa taron kasa da kasa na cika shekaru 100 da sake kafa makarantar hauza ta birnin Qum, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayin da yake bayyana abubuwa daban-daban na ayyukan da suka hau kan makarantar ya bayyana abubuwan da ake bukata na tabbatar da wani ci gaba mai cike da bunkasa da kuma ci gaba na yau da kullun, masu dacewa ga al'amuran da suka kunno kai, na wayewa, tare da ruhin ci gaba da gwagwarmaya da asalin juyin juya hali, da kuma iya tsara tsarin tafiyar da al'umma. Ya kuma jaddada cewa: Babban aikin makarantar hauza shi ne "bayyana hakikanin sakon musulunci", mafi kyawun misalai a cikinsu shi ne zayyana manya da kanana daga cikin wayewar Musulunci na zamani da gina al'umma, da yin bayani dalla-dalla ga al’adun musulunci.
Cikakken Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Shi Ne Kamar Haka;
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.
بسم الله الرّحمن الرّحیم
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, da mafificin salati da sallama ga shugabanmu Muhammadu Al-Mustafi da alayensa tsarkaka.
و الحمد لله ربّ العالمین و افضل الصّلاة و السّلام علی سیّدنا محمّد المصطفی و آله الطّاهرین سیّما بقیّة الله فی العالمین.
Bayyanar makarantar hauza ta Kum mai albarka a farkon karni na 14 bayan hijira wani lamari ne da ba a taba ganin irinsa ba wanda ya faru a cikin manya-manyan waki’oi masu ban tsoro. Abubuwan da suka sanya duhun yanayin yankin yammacin Asiya tare da jefa rayuwar al'ummar kasar cikin rudani da rugujewa.
Asalin da sanadin wannan yanayi mai ɗaci mai yaɗuwa da dawwama shi ne tsoma bakin ƴan mulkin mallaka da waɗanda suka yi nasara a yakin duniya na ɗaya, waɗanda suka yi amfani da duk wata hanya da nufin mamayewa da mallake wannan yanki mai ɗorewa mai cike da albarkatun ƙasa. Sun sami damar cimma burinsu ta hanyar karfin soja, makircin siyasa, cin hanci da karbar rashawa da daukar hayar maciya amanan cikin gida, farfaganda da kayan aikin al'adu, da duk wata hanya mai yiwuwa.
A Iraki, sun kafa gwamnatin Biritaniya, sannan suka kafa masarautun yan korensu; A yankin Levant, Ingila a gefe guda Faransa a dayan gefen sun fadada ayyukansu na mulkin mallaka ta hanyar kafa tsarin kabilanci a wani bangare da kuma mulkin dangin 'yan korensu na Burtaniya a daya bangaren, tare da haifar da zalunci da matsin lamba ga al'umma musamman musulmi da malaman addini a duk fadinsa. A Iran, sannu a hankali sun daukaka tare da dora wani Kazakh mara tausayi, mai hadama, mara mutunci a matsayin Firayim Minista sannan zuwa sarki. - A lokaci guda – A Palastinu anfarawa sahyoniyawa hijira sannu a hankali da basu makamai, tare da yin yunkurinsu sannu sannu suka shirya fagen samar da wata cutar daji a tsakiyar duniyar musulmi. A duk inda - ko a Iraki, Siriya, Falasdinu, ko Iran – zaka samu ana gwagwarmaya ga shirye-shireynsu na sun tarwatsa ssu, kuma a wasu garuruwa kamar Najaf, sun aikata lamarin wajen kame dimbin malamai, har ma da tura su gudun hijira ta wulakanci ga manyan mara’ji’oi irin su Mirza Na'ini, Sayyid Abul-Hasan Isfahani, da Sheikh Mahdi Khalisi, suka kaddamar da bincike gida gida domin su kama manyan Mujahidai. Al'ummai sun firgita, sun ruɗe, duhu ya kai kololuwarsa na rashin fata. A Iran, akwai Mujahidan Gilan, Tabriz, da Mashhad sun yi shahada, aka sanya masu kula da kwangiloli na yaudara a kan jagorancin al'amura.
A cikin irin wadannan yanayoyi masu daci da duhun dare ne tauraron Qum ya bayyana. Hannun ikon Ubangiji ya zaburar da wani babban malamin shari’a, mai tsoron Allah, kuma gogaggen malamin shari’a ya yi hijira zuwa Qum, ya rayar da Hauza da ta zama kufai wacce aka rufe ta, ya dasa wani sabon tsiro mai albarka a cikin dutsen da ke wannan zamanin da mai yuwa, kusa da hubbaren ‘yar Annabi Musa bn Ja’afar (amincin Allah ya tabbata a gare su) tsarkakakke kuma a cikin wannan kasa mai albarka.
Qum bata rasa manyan malamai ba a lokacin da Ayatullah Haeri ya iso; Manyan mutane irinsu Ayatullah Mirza Muhammad Arbab da Sheikh Abul Qasim Kabir da wasu da dama sun rayu a wannan gari, amma babbar fasahar kafa makarantar hauza shine ta zamo gidan reno da tarbiyar ilimi ga malamai da addini da imani (1), tare da dukkan kyawunta da tsare-tsarenta, ta zo ne kawai daga wata shaksiyya Mu’ayyid kamar Ayatullah Hajj Sheikh Abdulkarim Ha'iri (Allah ya kara masa daukaka).
Shekaru takwas da ya yi na kafa makarantar hauza da gudanar da karatun Hauza a birnin Arak, da shekaru kafin wadannan, kusancinsa da babban jagoran 'yan Shi'a, Mirza Shirazi a birnin Samarra, da kuma lura da dabarunsa na kafa da gudanar da makarantar hauza a birnin, ya ba shi shawarwari akan hakan. Kuma hikimarsa, jajircewarsa, kwadaitarwa, da begensa sun ciyar da shi gaba kan wannan tafarki mai wuyar gaske.
A farkon shekarunsa, tare da jajircewarsa ta gaskiya, makarantar hauza ta kubuta daga hannun takubban Reza Khani, wanda bai nuna tausayi ga karami ko babba ba a kokarinsa na goge alamomi da tushe na addini. Cikin sauki ya lalata mugun azzalumi, kuma Hauzar da ta kasance cikin matsananciyar matsin lamba na tsawon shekaru ta ci gaba da girma; Kuma daga gare ta ne, wata rana mai haske kamar Ruhullah ta fito. Makarantar hauza wacce dalibanta suka taba neman mafaka a kusurwoyin bayan gari da wayewar gari don ceton rayuwarsu, tare da yin karatu da muhawara a junnansu, da komawa cikin duhun dakuna a cikin makarantarsu da dare, a cikin shekaru arba'in da suka biyo baya, ta zamo cibiya ce da ta rura wutar gwagwarmaya da muguwar daular Reza Khan a duk fadin kasar Iran, tana kara raya zukata masu damuwa da rashin fata, tare da janyo matasa tsakiyar fagen wadanda aka mayar da su saniyar ware.
Kuma wannan makarantar hauza ne jim kadan bayan wafatin wanda ya assasasa ta da zuwan babban Marji’i mai girma Ayatullah Boroujerdi ta zama tsorouwar ilimi da bincike da isara da sakon shi'anci a fadin duniya. Kuma a karshe, wannan Hauzar ce dai, a cikin kasa da shekaru sittin, ta kara karfin ruhi da kimarsa, ta yadda za a iya kawar da gwamnatin mayaudara, lalatacciya, fasiqa da hannun alumma suka kawar da ita, bayan shekaru aru-aru, ta kafa Musulunci a matsayin mai mulkin siyasa na kasa mai girma, mai al’adu, mai cike da hazaka.
Wannan wanda ya fita daga wannan Hauzar ne mai albarka ya sanya Iran ta zama abin koyi na Musulunci a duniyar Musulunci, har ma ta zama ta farko ta addini a duk fadin duniya. Da bayani irin na annabta, jini ya yi nasara bisa takobi; Da hikimarsa Jamhuriyar Musulunci ta kafu. Da jajircewa da amanarsa al'ummar Iran sun kare kansu daga barazanar da suke fuskanta tare da cin galaba da yin fice a kan wau. Kuma a yau, da darasinsa da abin da ya bari, kasar nan tana wargaza shingaye da samun ci gaba a fannonin rayuwa da dama.
Rahma da yardan Allah su ci gaba da tabbata ga wanda ya assasa wannan al'umma mai albarka da daukaka da wannan bishiyar ilimi mai albarka. Mutum mai daraja, haziki, mai albarka, malamin addini da aka kawata shi da nutsuwa ta yakini, mai girma Ayatullah Hajj Sheikh Abdulkarim Haeri.
A yanzu ya zama wajibi a ce wani abu kan wasu ‘yan batutuwa da ake kyautata zaton suna da alaka da makarantar hauza a yau da kuma gobe, da fatan za su taimaka wa makarantar hauza mai nasara a halin yanzu wajen isa ga matsayin Hauza na zama makarantar hauza mai “ci gaba da yin fice”….
Zamu ci gaba Insha Allah
Your Comment