11 Ga Watan Zul-Ka'adah A irin wannan rana ce a Shekara ta 148 bayan hijirah aka haifi Imamu Ali Ar-Ridha (as) a Garin Madinah, wato a Shekarar da Kakansa Imamu Sadiq (as) ya yi Shahada. Shi ne Imami na 8 daga jerin Limaman Shiriya 12 da Ma'aiki (Saww) ya ce Mu yi riko da Su a bayansa.
Mahaifinsa Shi ne Imamu Musa bin Ja'afar Al-Kazimu (as).
Mahaifiyarsa kuwa Ummu Walad ce, ana kiran ta da Ummul banin, ko Sayyidah Najmah, ko Tuktam, amincin Allah ya kara tabbata a gare ta.
Ya zo a ruwaya cewa: As-Sayyidah Hamidah al-barbariyya Mahaifiyar Imamu Musal Kazim (as) ita ce ta siyo Sayyidah Najmah (as) a matsayin Kuyanga, sai ta yi Mafarki da Manzon Allah (Saww) yana gaya mata cewa: "Ya ke Hamidah, ki bayar da Najamah ga Danki Musa, lallai za ta haifa masa mafi alkhairin mutanen da ke doron kasa". Sai kuwa ta bayar da Sayyida Najmah ga Danta Imamu Musal Kazim (as), a lokacin da ta haifa Masa Imamu Ar-Ridha (as) sai ya kira ta da Sunan: Ad-Dahirah".
An ruwaito daga Sayyidah Najmah Mahaifiyar Imamur-Ridha (as) ta ce: "A lokacin da na dauki cikin Dana Ali, ban ji wani nauyin ciki ba, kuma na kasance a cikin baccina ina jin sautin Tasbihi da Hailala da Tamjidi a cikin Cikina!, sai in ji firjici da tsoro kan wannan!, idan na farka kuma sai in daina jin komai!, a lokacin da na haife Shi kuwa sai ya sauko a Kasa yana mai dora Hannunsa a Kasa, yana daga Kansa a Sama yana motsa Lebensa kamar yana Magana, sai Babansa Musa bn Ja'afar (as) ya shigo, ya ce: "Ina taya Ki murna ya Najmah!, wannan girmama wa ce daga Ubangijinki". Sai na mika masa Shi a cikin wani farin Kyalle, sai ya yi masa Kiran Sallah a Kunnensa na Dama, ya kuma yi masa Ikama a Kunnen Hagu, sannan ya yi masa addu'a a cikin Ruwan Furat, ya gunda a baki ya saka masa. Sannan ya mayar mini da Shi (Jaririn) yace: Karbe Shi, lallai Shi Bakiyyatullahi ne a doron Kasa".
Alkunyar Sa: Ana yi masa alkunya ne da Abul Hasan.
Wasu Daga Cikin Lakubbansa:
Imam (as) yana da Lakubba masu tarin yawan gaske, amma ga wasu daga ciki:
Siraajullahi, Nurul huda, Kurratu ainil Mu'uminin, Makidatul mulhidin, Kuf'ul Maliki, Kaafil Khalki, Rabbus-Sarir, Ri'abut-Tadbiri, Al-Faadilu, As-Saabiru, As-Siddiku, Ar-Radiyyu, al-Garibu, Ar-Ra'ufu, Kafiilul Gazaal, sai kuma wanda ya fi Shahara, wato AR-RIDHA (as).
Dalilin Yi Masa Lakabi Da Ar-Ridha.
Ibnu Babuwaihi ya Ruwaito da Isnadi mai kyau zuwa ga Bazandiy ya ce:- Na ce da Abi Ja'afar (Imam Jawad as) : Hakika wasu Mutane daga wadan da ba su tare da Ku suna cewa: Lallai Babanka an Kira shi ne da AR-RIDHA saboda yardar sa da Wilayatul Ahad dinsa.
Sai Imam (as) ya ce:- Wallahi sun yi karya, sun yi Fajirci, Allah Swt ne ya Kira shi da AR-RIDHA, saboda ya kasance Yardajjen Allah a Samansa, kuma a Kasansa ya yarda da Manzonsa da Aimma a bayansa amincin Allah ya tabbata a gare Su.
Bazandiy ya ce: Sai na ce: Ashe kowanne daya daga Iyayenka da suka shude bai kasance ya yarda da Allah da Manzonsa da Aimma ba a bayansa?
Sai ya ce:- Haka ne. Sai na ce:- To me ya sa shi aka kira Baban naka da AR-RIDHA a tsakanin su?.
Sai ya ce:- Saboda Shi Mukhalifuna (Wanda ba Shi'a ba) na daga Makiyansa sun yarda da Shi, kamar yanda Muwafiqun (Shi'a) daga Masoyansa suka yarda da Shi, Kuma wannan bai kasance ba ga wani daga cikin Iyayensa amincin Allah ya tabbata a gare Su, saboda haka aka kira shi da AR-RIDHA a tsakanin Su".
Rubutun Zobensa: A jikin Zoben Imam a.s an rubuta:- "Masha'Allahu, wala kuwwata illa billahi".
Sarakunan Da Ya Yi Zamani Da Su.
Sarakunan da ya yi Zamani da Su sun hada da: Haruun Al-abbas, wanda ake kira da Rashid, Al'amin Al-abbasi, da kuma Ma'amun Al-abbasi, wanda shi ne ya shahadantar da Imam (as).
Tsayin Muddar Imamancin Sa: Tsayin Imamancinsa Bayan Mahaifinsa, Shekaru 20 Ne
Shekarun Sa A Duniya:- Shekaru 55.
Shahadar Sa:- Imam (as) ya yi Shahada ne a Garin Dus da ke Khuraasan, a shekara ta 203 bayan hijira.
Makashin Sa:- Al-Ma'amun al-Abbasiy ne ya Shahadantar da Shi da guba a cikin Inibi.
Kissar Imamu Ar-Ridha (As) Da Barewa......
@Ishaq Muhammad Ishaq.
Your Comment