Martanin kungiyar Ansarullah ta Yaman kan hare-haren da Isra'ila ta kai musu
A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Mohammed Al-Bakhiti ya jaddada cewa: Makomar da Amurka da gwamnatin sahyoniyawa suke yi na kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula na nuni da gazawarsu da cin galaba a kansu.
Al-Bakhiti ya kara da cewa: Muna sanar da Birtaniya, Amurkawa, da sahyoniyawa cewa, zamu ci gaba da ayyukan sojinmu na ci gaba da taimakawa Gaza, ba tare da la'akari da irin halin kuncin da wannan sadaukarwa zata haifar ba.
Wannan mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: Muna gaya musu cewa su jira martanin Yaman. Ya kuma ce: Hare-haren baya-bayan nan ba shi da wani tasiri kan matakin goyon bayan al'ummar kasar Yemen kan aikin tallafawa Gaza.
Wannnan babban jami'in kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: Sahayoniyawa sun tsallaka jajayen layukan da suka dace, kuma dole ne su jira martanin Yemen.
Al-Bakhiti ya kara da cewa: Kowa ya san cewa Amurkawa da Birtaniya da yahudawan sahyoniya sun yi ruwan bama-bamai a wuraren fararen hula a wadannan hare-haren, kowa ya san wannan lamari.
A yayin da yake yin watsi da zargin da akewa Iran na hannu a harin da kungiyar Ansarullah ta yi tare da dogaro da Iran ya bayyana cewa: Suna kokarin dangana aikin goyon bayan kasar Yemen da dogaro da Iran, amma sai mu ce dogaronmu yana kan gwagwarmayar Palastinawa ne.
Ya kara da cewa dukkanin hare-haren soji da kasar Yamen ta kai kan gwamnatin sahyoniyawa ana gudanar da su ne ta hanyar hadin gwiwa kai tsaye da kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa musamman Hamas da Jihad Islami, wani lokacin kuma bisa bukatarsu.
Al-Bakhiti ya jaddada cewa: Kasar Yemen a shirye take ta fuskanci dukkan al'amuran da Amurka, da gwamnatin Sahayoniya da Birtaniyya suka tsara. A shirye muke mu yi yaƙi a dukkan bangarorin uku.
Yayin da yake ishara da harba makami mai linzami da kasar Yemen ta yi a baya-bayan nan, ya ce: “Abin mamakin makiya shi ne saboda makamin da muka yi ya ratsa ta dukkan matakai hudu na kariyar tsaro ta sama kuma yana da karfin fashewa da ya ba su mamaki.
Al-Bakhiti ya kuma nuni da cewa: Sahayoniyawa suna kokarin kafa sabbin rigingimu daga Yemen zuwa Lebanon. Amma muna sanar da su cewa, Ansarullah ba za ta bari gwamnatin sahyoniyawa ta kafa ka'idojin fadan ba a yankin ba, ko kuma ta canza fuskarta yadda ta ga dama, kuma mu ne za mu yi amfani da ka'idojin fadan.
Ya kammala da sanar da cewa: Asarar da makiya suka fuskanta ya fi na kasar Yemen din.
A yammacin talata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wani hari ta sama a tashar jiragen sama na kasa da kasa da ke Sanaa babban birnin kasar Yaman.
Majiyoyin yada labaran Isra'ila sun ce an kai hare-hare ta sama akalla 15 a filin jirgin saman Sanaa.
Sojojin Isra'ila sun kuma yi ikirarin cewa sun yi nasarar "katse" filin jirgin saman Sana'a gaba daya a hare-haren da ta kai a Yemen. Sanarwar ta kuma yi ikirarin cewa kungiyar Ansarullah na amfani da wannan filin jirgin wajen jigilar makamai.
Bayan kai wadannan hare-hare, sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa an lalata dakin taro, jiragen sama, da na farar hula na filin jirgin sama na Sanaa.
Kakakin rundunar sojin Isra'ila a yayin da yake jaddada ci gaba da aiyukan ta’addancin da suke yi a yankin na Yemen, ya kara da cewa: Haka nan kuma an kai hare-haren a wasu tashoshin samar da makamashi da dama da ke kusa da birnin Sanaa.
Tashar talabijin ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta Channel 12 ta sanar da cewa, gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar jami'an soji da na siyasa na Amurka ne suka kai hare-haren.
Kafar yada labaran yahudawan sahyuniya ta nakalto jami'an soji na gwamnatin kasar na cewa jiragen sama 30 ne suka shiga cikin harin da aka kai a kasar Yaman kuma an gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar Amurka.
Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta ayyana wani gagarumin shiri na tunkarar hare-haren kungiyar Ansarullah a kan yankunan da ta mamaye.
Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin mamaya, ta nakalto majiyar soji, ta sanar da cewa, Tel Aviv na jiran martanin kungiyar Ansarullah, kuma a saboda haka ta ci gaba da wayar da kan jama'a a tsarin tsaronta na sama. Sannan wani babban jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi ikirarin cewa za a ci gaba da kai hare-hare ta sama kan kasar Yaman.
Your Comment