7 Mayu 2025 - 11:07
Source: ABNA24
Pakistan A Musayar Wuta Tsakaninta Da Indiya, Ta Tabbatar Da Kame Sojoji Da Kabo Jiragen Sama.

Kakakin rundunar sojin Pakistan na cewa, an tafka ruwan bama-bamai a wurare da dama na kan iyakar kasashen biyu, a yayin da hukumar ta ambato sojojin Indiya na cewa fararen hula 10 ne suka mutu yayin da wasu 35 suka jikkata a harin da Pakistan ta kai a yankin Kashmir.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: ana ci gaba da yin luguden wuta tsakanin Indiya da Pakistan a mafi yawan layin tsagaita bude wuta a yankin Kashmir bayan da Indiya ta yi ruwan bama-bamai a wurare 9 a cikin Pakistan a daren jiya tana mai ce kayayyakin more rayuwa ne na 'yan ta'adda da suka kai hari da makami a Kashmir a watan jiya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin sojin Pakistan yana cewa an tafka luguden wuta a wurare da dama a kan iyakar kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rundunar sojin Indiya cewa, an kashe fararen hula 10 tare da jikkata wasu 35 a harin da Pakistan ta kai a yankin Kashmir.

A halin da ake ciki kuma, kakakin rundunar sojin Pakistan, Janar Ahmed Rashid, ya tabbatar da mutuwar fararen hula 26, yayin da wasu 46 suka jikkata, a hare-haren da sojojin Indiya suka kai mataki na biyu, kan wasu wurare shida a cikin Pakistan.

Tun da farko kakakin babban magatakardar MDD António Guterres ya ce babban sakataren ya damu matuka game da hare-haren da sojojin Indiya ke kaiwa Pakistan da kuma yankin Kashmir da ke karkashin ikon Islamabad, kuma ya yi kira ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa a kokarinsu na soji, saboda duniya ba za ta iya daukar wani fadan soji tsakanin kasashen biyu ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha