Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Biyo bayan faduwar wannan gwamnati Bashar Assad ya bar birnin Damascus
Kungiyoyin 'yan adawa masu dauke da makamai da suka hada da kungiyar Tahrir Sham da kawayenta, a hukumance sun sanar da faduwar gwamnatin wannan kasa karkashin jagorancin Bashar Assad a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
A cikin wannan sanarwa, an jaddada cewa, wajibi ne dukkanin kungiyoyi da mutane masu dauke da makamai su kiyaye hadin kai da diyaucin kasar Siriya, da kare dukkan 'yan kasar da dukiyoyinsu, da sake gina gwamnati bisa 'yanci da adalci, da samar da cikakken sulhu na kasa, da mayar da 'yan gudun hijira, da mayar da martanin da ya kamata ga duk wadanda suka aikata laifuka kan al'ummar Siriya su yi kokari su ba da hadin kai.
Yunkurin Hadin gwiwar tsohuwar gwamnatin Siriya da 'yan adawa masu dauke da makamai
Muhammad Ghazi Jalali, tsohon firaministan kasar Syria, ya sanar ta hanyar fitar da wani faifan bidiyo da aka nada a gidansa, cewa zai bayyana a ginin firaministan kasar da ke birnin Damascus a safiyar yau Lahadi, kuma zai dauki matakin da ya dace na mika mulki.
Makomar Bashar Assad
A gefe guda kuma, hambararren shugaban kasar Syria Bashar Assad, ya bar wannan birnin zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba kafin faduwar Damascus. Wasu kafafen yada labarai na cewa jirgin da ke dauke da Bashar Assad ya bace a lardin Homs, wasu kafafen yada labaran kuma na cewa ya kai wani guri a wajen kasar Siriya.
Firayim Ministan Siriya: A shirye nake in mika mulki
"Muhammed Jalali", Firayim Ministan Siriya:
Ina fata sabon tsari mai kyau ya fara ga Siriya. Muna mika hannunmu ga ‘yan kasar Syria, muna rokon kada su lalata dukiyar jama’a.
Mu a shirye muke da duk wani matsaya da al'ummar Siriya za su dauka, kuma a shirye nake in ba da hadin kai ga duk wani shugaba da al'ummar Siriya suka zaba.
Siriya gidana ce kuma zan zauna a gida na kuma a shirye nake da in goyi bayan ci gaba da harkokin gwamnatin rikon kwarya.
Mun yi imanin cewa, Siriya ta kasance ga dukkan mutanen Siriya kuma za ta iya kulla kyakkyawar dangantaka da dukkan kasashe makwabta.
