3 Disamba 2024 - 12:31
Falasdinawa 36 Sukai Shahada A Hare-Haren A Yau A Zirin Gaza

Majiyoyin ma'aikatar lafiya sun sanar da cewa ya zuwa yanzu Falasdinawa 36 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza a yau.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Wanda bayan wannan harin Adadin shahidai a Gaza ya karu zuwa 44,502

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, mutane 105,454 suka jikkata.

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata sojojin mamaya sun sake yin kisan kiyashi sau 2 kan fararen hula a wannan yanki, inda Falasdinawa 36 suka yi shahada tare da jikkata mutane 96.