1 Disamba 2024 - 06:31
Isra’ila Ta Kara Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Karo Na 62 A Lebanon; Bayyanar Jiragen Sama Marasa Matuka A Beirut

Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah har sau 24 a ranar Asabar din da ta gabata, kuma ta haka ne adadin karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ya kai sau 62 tun bayan farawarta a ranar Laraba

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton cewa, an samu wasu shahidai biyu da kuma wasu 2 da suka samu raunuka a sabon harin da gwamnatin Sahayoniyya ta kai a garin Nabatie da ke kudancin kasar Labanon

A cewar jaridar Al Arabi Al-Jadeed, gwamnatin yahudawan sahyoniya ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah har sau 24 a ranar Asabar din da ta gabata, kuma ta haka ne adadin karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ya kai sau 62 tun bayan farawarta a ranar Laraba.

Tel Aviv ta sake keta yarjejeniyar tsagaita wuta a yau ta hanyar Jiragen leken asiri da ke tashi a Beirut

Jiragen leken asiri na gwamnatin Sahayoniya sun yi ta tashi a kurkusa a birnin Beirut da yankunan kudancin kasar a safiyar yau Lahadi.

A cewar wannan rahoto, jiragen da aka ambata sun karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da Lebanon.