1 Disamba 2024 - 06:19
Biranen 'Yan Shi'a Na Nubl Da Al-Zahra A Arewacin Siriya Sun Fada Hannnun ‘Yan Ta’adda

Garuruwan Nubl da Al-Zahra sun kasance mazaunin kusan mutane 60,000 na 'yan Shi'a Isna Ashariyya na kasar Siriya, kuma a ko da yaushe wadannan garuruwa biyu na Shi'a suna fuskantar hare-hare daga kungiyoyin takfiriyya tun farkon rikicin kasar Siriya.

'Yan ta'addar takfiri sun mamaye Garuruwan 'yan Shi'a na Nubl da Al-Zahra.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton cewa, mayakan takfiriyya sun mamaye garuruwan Nubl da Al-Zahra na ‘yan shi’a a yankin arewacin lardin Halab da ke arewacin kasar Siriya.

Mazauna wadannan garuruwa biyu na ‘yan Shi’a sun bar Nubl da Al-Zahra kafin faduwar wadannan garuruwan, inda suka nemi mafaka a wasu yankunan kasar Siriya.

'Yan ta'addar takfiriyya bayan sun mamaye garuruwan Nubl da Al-Zahra na Shi'a sun lalata gidajen 'yan Shi'a a wadannan garuruwa.

Bayan da 'yan ta'adda suka mamaye birnin na Halab, kungiyoyin 'yan ta'adda garuruwan sun mamaye garuruwan Nubl da Al-Zahra gaba daya, inda aka tilastawa mazauna wadannan garuruwa barin gidajensu domin ceto rayukan kananan yara da matan Shi'a.

Garuruwan Nublda Al-Zahra sun kasance mazaunin kusan mutane 60,000 na 'yan Shi'a Isna Ashariyya na kasar Siriya, kuma a ko da yaushe wadannan garuruwa biyu na Shi'a suna fuskantar hare-hare daga kungiyoyin takfiriyya tun farkon rikicin kasar Siriya.