Sheikh Naim Qassam, babban sakataren kungiyar Hizbullah:
Dukanmu mun ga mutanen Lebanon waɗanda suka koma ƙauyuka da garuruwansu kai tsaye bayan tsagaita wuta. Kun ga sun yi magana a kan wata babbar nasara, kowannensu ya ambaci gidan da aka ruguje, da kauye da aka ruguza, da shahidan iyalansa, amma duk da haka sun ce gwagwarmaya ta yi nasara, kuma tafarkin Nasrullah (Shahidi) ya yi nasara kuma mun yi nasara.
Matsayin da kungiyar Hizbullah ta dauka ya sanya sojojin Isra'ila suka firgita kuma duk wannan ya sa Isra'ila ta daina kai hare-hare ba tare da cimma manufarta ba.
Ba mu son yaƙi, amma muna son taimaka wa Gaza kuma a shirye muke mu yi yaƙi idan aka kakaba mana yaƙi.
Kungiyar Hizbullah ta dawo da karfinta ta kuma karbe ragamar tafiyar da harkokinta tare da kafa tsarin umarni da sarrafawa.