28 Nuwamba 2024 - 12:03
Isra'ila Ta Karya Sulhun Tsagaita Wuta A Kudancin Lebanon / sojojin Isra'ila Sun Kai Hari Kan 'Yan Gudun Hijira

A cewar kamfanin Irana Wasu majiyoyin labarai sun rawaito cewa sojojin mamaya da su kai matukar fusata da komawar mazauna kudancin Lebanon gidajensu sun kai musu hari. Isra'ila Ta Karya Sulhun Tsagaita Wuta A Kudancin Lebanon / sojojin Isra'ila Sun Kai Hari Kan 'Yan Gudun Hijira

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: A cewar kamfanin Irana Wasu majiyoyin labarai sun rawaito cewa sojojin mamaya da su kai matukar fusata da komawar mazauna kudancin Lebanon gidajensu sun kai musu hari.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera a yau Alhamis cewa: a yayin da mazauna kudancin kasar Labanon ke komawa gidajensu bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, hakan bai yi wa sojojin yahudawan dadi ba.

Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya ta bayar da rahoton cewa, wasu 'yan kasar Lebanon biyu sun jikkata sakamakon harin da jirgin da gwamnatin Isra'ila ya kai kan wata mota a kudancin kasar Labanon.

Wasu majiyoyin labarai sun kuma bayar da rahoton cewa, an jikkata mutane uku a wani hari da aka kai kan wata mota a garin Misra da ke kudancin kasar Lebanon.

Shi ma wakilin Al-Mayadeen a Bent Jbeil da ke kudancin kasar Lebanon ya ba da rahoton komawar 'yan gudun hijirar zuwa wannan birni mai dimbin yawa, inda aka yi ta gwabza kazamin fada tsakanin mayakan gwagwarmaya da na yan mamaya.

Har ila yau, wakilin Al-Mayadeen ya bayar da rahoton cewa: An tsamo gawawwakin wasu shahidan Hizbullah da na Amal a Jalahiyya, wadanda suka sha gwabza kazamin fada a kwanakin karshe na yakin.

A daya bangaren kuma, 'yan kasar Labanon da suka dawo daga Sham ta mashigar "Al Masan" sun ce: Idan ba don mayakan gwagwarmaya da jinin shahidai ba, ba za mu iya komawa kasarmu ba.

Wakilin Al-Mayadeen a cikin "Al-Khayyam" ya kuma bayar da rahoto game da fargabar da sojojin yahudawan sahyoniya da ke cikin garuruwan kan iyaka da 'yan gudun hijirar suka shiga duk kuwa da rufe hanyoyin shiga.

Gidan radiyon yahudawan sahyoniya ya bayyana cewa, makasudin ci gaba da kai hare-hare ta sama da harbin da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi kan mazauna kudancin kasar Lebanon shi ne don hana su dawowa da kuma korar mazauna yankin.

Majiyar sojojin kasar Labanon ta kuma bayyana cewa: Manufar hare-haren da makiya Isra'ila ke kaiwa garuruwan da ke kan iyaka shi ne hana mazauna wadannan garuruwa dawowa duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma makiya suna son wadannan yankuna su ci gaba da kasancewa a ƙone cikin yaƙi.

A halin da ake ciki, majiyoyin yankin na kasar Labanon sun bayyana cewa, an yi harbe-harbe a garin "Ramish", wanda a sakamakon haka, an lalata wani gida da wani shago.

Wadannan majiyoyin sun ba da rahoton motsawar jiragen yaƙi a saman kudancin Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a daren Talata ne Amurka ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da kungiyar Hizbullah bayan shafe tsawon watanni ana yakin.

Bayan da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kasar Labanon da gwamnatin sahyoniyawa, wannan yarjejeniya ta fara aiki da safiyar Laraba.

A cewar Biden, ya kamata sojojin gwamnatin sahyoniyawan su janye daga kudancin kasar Lebanon sannan sojojin Lebanon za su jibge a kan iyakokin wannan kasa da kuma Falasdinun da aka mamaye.

Sojojin yahudawan sahyoniya suna harbin 'yan jarida a birnin Khayyam na kasar Lebanon

Duk da tsagaita bude wuta, wata motar buldoza ta sojojin Isra'ila ta toshe hanyar da ke tsakanin arewacin Khayam da tsakiyar wannan birni. Yayin da 'yan jarida ke daukar hoton motsawar wannan buldoza sojojin Isra'ila sun harbe su tare da kore su daga wurin.