27 Nuwamba 2024 - 09:57
Sahayoniyawa: Sojojin Isra'ila Sun Sha Kaye A Yakin Da Suke Yi Da Lebanon + Bidiyo

A Lokaci Guda Tare Da Farkon Tsagaita Wutar; Yadda Yahudawan Sahyoniya Suke Bakincinkin Dawowar ‘Yan Lebanon Zuwa Kudu/ Me Ya Sa Gwamnatin Sahyoniyawan Ta Amince Da Tsagaita Bude Wuta?!

A daidai lokacin da aka fara tsagaita wuta a kasar Labanon, mutanen da suka rasa matsugunansu na yankuna daban-daban da suka hada da mutanen kudanci, Bekaa da Beirut, sun fara komawa gidajensu. Fitowar hotuna daga wannan dawowarsu ya sa yahudawan sahyoniya jin haushi.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa: a daidai lokacin da aka fara tsagaita bude wuta a kasar Labanon, mutanen da suka yi gudun hijira daga yankuna daban-daban da suka hada da mutanen kudancin kasar, Bekaa da Beirut, sun fara komawa gidajensu.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin kasar Labanon da gwamnatin yahudawan sahyuniya ta fara aiki a yau Laraba da misalin karfe 4:00 na safe agogon birnin Beirut (05:30 agogon Tehran).

A sa'i daya kuma, mataimakin shugaban majalisar siyasa ta kungiyar Hizbullah ya jaddada wajibcin yin la'akari da ra'ayin kungiyar game da tsagaita bude wuta, ya kuma ce wasu sharuddan da kafafen yada labaran Isra'ila suka watsa a kan wannan yarjejeniya ba daidai ba ne.

"Mahmoud Qumati" ya fayyace cewa: Hizbullah ba ta amince da alkawuran Netanyahu ba kuma ba za ta fada tarkon sa ba.

A cewar rahoton kafar Larabci ta 21, Mahmoud Qumati ya kuma bayyana cewa: Dalilin da ya sa muke shakkar da kin amincewa da Netanyahu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, shi ne ya yaudare mu a koyaushe.

Sahayoniyawan: Sojojin Isra'ila Sun Sha Kaye A Yakin Da Suke Yi Da Lebanon

A sa'i daya kuma, kafofin watsa labaru na yahudawan sahyoniya, bisa hotunan da aka watsa na komawar mutane Labnon zuwa kudancin kasar, sun dauki wannan matakin a matsayin cikakkiyar nasara ga kungiyar Hizbullah, tare da rubuta cewa: Dukkan hotunan da bangaren Lebanon ya watsa bayan tsagaita bude wuta na nuni da komawar 'yan gudun hijira daga wancan gefe zuwa gidajensu; Wannan yana nufin cikakkiyar nasara. Me ya sa ba a buga hotunan mutanen da suka koma gidajensu a arewa ba?!

Kamar yadda binciken gidan talabijin na 12 na gwamnatin sahyoniyawan ya nuna dangane da yarjejeniyar da kasar Labanon; Kashi 69% na sahyoniyawan sun yi imanin cewa Isra'ila ba ta yi nasara a wannan yaki da Hizbullah ba.

Rahotanni daga kasar na cewa, bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Netanyahu ya yi, sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun janye daga wasu yankunan kudancin kasar ta Lebanon da suka hada da kauyukan Shama da Tayirharfa, kuma al'ummar kudancin kasar Lebanon na komawa garuruwa da gidajensu.

Wannan Babban Nasara Ce

Shi ma Abdulbari Atwan, sanannen manazarcin Larabawa kuma manajan kamfanin Rai Alyoum, ya bayyana cewa: A karon farko a tarihi, jaruman Hizbullah ne suka samu wannan nasara; Fiye da rokoki 350 sun afkawa garuruwan Isra'ila, babban nasara ne; Isra'ilawa kuwa saboda sun nutse sun sha kashi, nan da nan suka amince da yarjejeniyar.